Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ta bayyana cewa gobara ta ci dakunan dalibai mata, har dakuna 30 a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Wudil, Jihar Kano.
Kakakin Yada Labarai na hukumar, Saidu Mohammed ne ya bayyana haka yau ga Kamfanin Dillancin Labarai, NAN.
Ya ce wutar ta tashi ne misalin karfe kafin 9 na dare, inda wani mai suna Alhaji Sagir ya buga musu waya, da karfe 9:52 ya sanar da su tashin gobarar.
Mohammed ya kara da cewa sun isa wurin karfe da 10:21, kuma suka yi nasarar kashe gobarar.
Ya yi karin hasken cewa baya ga dakunan kwana 30 na dalibai mata, wutar ta kuma lashe ban-dakuna 20 da dakuna 4 na dafa abinci duk a bangaren.
Sai dai kuma ya ce an auna arziki domin ba a yi asarar rayuka ba, tunda dukkan dalibai su na gida, saboda yajin aikin da malaman jami’o’i ke yi, tun daga ranar 4 Ga Nuwamba, 2018.
Kakakin ya ce an alakanta gobarar daga wurin da aka hada wayoyin bangaren wutar saman benen da ya ci wutar.
Discussion about this post