A mazabar tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, jam’iyyar PDP ta yi rata mai tsawo ga jam’iyyar APC, yayin da ta samu kuri’u 225, ita kuma APC ta tashi da kuri’u 82.
Haka wannan sakamakon ya nuna a mazabar ta Afao 1, Irepodun a Ekiti.
Sauran jam’iyyu ANDP, NIP, RBNP, SNC, da UPN duk sun samu kuri’u daya kowace. DPP kuri;a 2, ita kuma PCP kuri’a 3.
Fayose gogarman dan PDP ne da ya ke nuna tsananin adawa da buhari tun a zaben 2015.
Kokarin da ya yi na dora dan gaban goshin sa a kan mulkin jihar Ekiti bayan ya kammala na sa wa’adin bai yi nasara ba, domin ya sha kaye a zaben da jama’a da dama suka tabbatar da cewa an yi amfani da karfin jami’an tsaro.