Hukumar Kula da Masu Hijira ta Duniya (IOM), ta yi matukar nuna damuwar ta dangane da yadda aka samu yawaitar munanan hare-haren Boko Haram daga watan Nuwamba, 2018 zuwa yau.
IOM ta ce daga Nuwamba zuwa wannan makon, Boko Haram sun raba mutane sama da 59,000 daga gidajen su.
Har ila yau dai, kungiyar ta ce a cikin wadannan watanni uku, Boko Haram sun kama garuruwa da dama. Wannan kungiya ta bayyana haka a birnin Geneva, cewa an kara samun wadannan hare-hare ne da kuma yawaitar masu gudun hijira, saboda sabbin muggan makamai na zamani da Boko Haram ke amfani da su a yanzu.
IOM ta ce a baya Boko Haram ya takaita ne a Barno da Yobe da kuma Adamawa. Amma yanzu matsalar ta mamaye dukkan kasashen da suka yi iyaka da Tafkin Chadi.
Frantz Celestin, wanda shi ne babban jami’in IOM a Najeriya, ya kara da cewa talakawa fararen hula su ke ta dandana kudar makaman Boko Haram, dpmin su ake ta kashewa, ake sacewa, ake kona wa garuruwa kuma ake tilasta su yin gudun hijira.
Sannan kuma ya yi tsinkayen cewa sojoji sun fatattakar Boko Haram a farkon Nuwamba ne saboda matsalar tsananin hazo a yankin Arewa ta Tsakiya, saboda tsananin hunturu.
“Da Boko Haram suka kai hari a hari a garin Rann, na su kyale kowa ba. Sun kashe jama’a, sun kone ofishin MSF, sun kone asibitin UNICEF. Har da ginin WHO/ICRC duk sai da suka kai wa hari.”
Majalisar Dinkin Duniya ma a cikin wani rahoton ta, ta ce an kashe sama da mutane 27,000 a jihohi uku na Arewa maso Gabas, an kuma sace dubban mata da kananan yara.