Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’I ya haramta wa kungiyoyin sa kai na bijilante da Kato-da-gora fitowa da yin aiki a lokacin zabe.
El-Rufai ya ce abinda za su yi a ranar zabe shine su fito su jefa kuri’a sannan su karkade kafafuwan su su koma gida kamar yadda sauran mutane za su yi.
El-Rufa’I yace jami’an tsaro ne za su samar da tsaro a lokacin zabe a duk fadin jihar da suka hada da ‘yan sanda, Hukumar kula da shige da ficin a kasa(NIS), jami’an Kwastam, jami’an hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), NSCDC da KASTELA.
Ya sanar da haka ne wa manema labarai ranar Juma’a inda ya kara da cewa a ranar Asabar da za ayi zabe masu gadin mayan ma’aikatan gwamnati ma baza su yi aiki ba.
Gwamnati ta dauki wannan shawara ne a dalilin zargin da jam’iyyar PDP ta yi mata cewa wai za ta yi amfani da kungiyar bijilante da ‘yan Kato- da- Gora da sauran ‘yan kungiyoyi irin su a lokacin zabe a jihar domin yin magudi.
A karshe gwamna El-Rufai ya yi kira ga mutanen jihar da su nisanta kansu daga duk wani abu da zai tada zaune tsaye a lokacin zaben.