EL-CLASICO: Vinicious ya nuna wa duniya cewa mai kamar zuwa ake aike

0

Dan wasan Barcelona Malcom ya ci kwallon da ya fitar da Barcelona daga fargaba, sannan kuma ya nuna wa mai horas da Barcelona, Valverde cewa ajiye shi da ake yi benci asara ce.

Malcom ne ya rama wa Barcelona cin kwallo daya da Real Madrid ta yi mata a Camp Nou a daren jiya, a wasan farko na kusa da na karshe a Kofin Copa Del Rey.

Real Madrid ta baras da kwallaye, domin kamata ya i a ce ta yi nasara a kan Barcelona, ba wai a tashi kunnen doki da ci 1-1 ba.

Sabon dan wasan Real Madrid, karamin yaro dan shekara 18, mai suna Vinicious, za a ce ya fara buga gasar gwani na gwanayen ‘yan kungiyar Madrid da na Barcelona, wanda ake fi sani da El-Clasico.

Ana kiran kowace karawa da kungiyoyin biyu za su yi da suna El-Clasico, saboda kallon da ake yi wa su biyu din cewa a duniyar kwallo babu kamar su.

Vinicious shi ne dan wasa mafi kankantar shekaru ko daga bangaren Real Madrid ko daga Barcelona da ya taba buga wasan El-Clasico a cikin wannan karni na 21.

Ya nuna cewa shi yaro ne kuma dan aiken da duk inda Madrid za ta tura shi, to zai iya zuwa cikin sauri ya kai sakon kwallo a ci, kuma Madrid ta yi nasara.

Minti 6 da fara wasa Vinicious ya yi aikin nasa, inda ya bai wa Lucas Varquez kwallo, shi kuma ya sheka ta cikin ragar Barcelona.

Tsohon mai horas da Madrid da aka kora bayan Barcelona ta ci Madrid 5-1, Lepaturgi, ya yi wa Vinicious kallon raina kama ka ga gayya. Shi ya sa ya rika ajiye shi a benci.

Amma zuwan Santiago Solari, sai ya rika amfani da shi, kuma ya rika biya masa bukatar yin irin wasan da ya ke so ya yi.

Barcelona ta rama kwallon ta bayan dawowa hutun rabin lokaci. Sai dai kuma ana garin da saura rina a kabar kowanen su.

Idan Madrid ta na so ta tsira da mutuncin ta, to ta yi nasara a kan Barcelona, kuma ta yi nasara a wasan karshe ta ci kofi kawai.

Wannan ne zai zama wata alamar cewa mai horaswa Santiago Solari shi ma da gaske ya ke yi, kamar yadda Znedine Zidane ya karbi koyarwar kungiyar har ya yi nasarar cin Kofin Zakarun Turai sau uku a jere.

Ko Barcelona ta yi nasara a kan Madrid, daukar Copa Del Rey ba zai zame mata abin alfahari ba, domin babban abin da ya fi damun kungyar shi ne rashin daukar Kofin Zakarun Turai da ba ta yi ba har tsawon shekara hudu, wanda Madrid ke yin nasara sau uku a jere.

Akwai wasannin El-Clasico biyu da kungiyiyin za su sake karawa kwanan nan, kuma duk a gidan Madrid. Lallai masu kallo ba za su gaji da kallon lailaya kwallo, ba kuma za su gaji da kallon yadda ake mugunta da hatsaniya har da tofa juna miyau ba.

El-Clasico kenan, ga taka leda, ga keta kuma rigima, har ma da dabanci.

Share.

game da Author