Wani jigo a jam’iyyar PDP na jihar Kaduna da shine darektan yada labaran jam’iyyar, ya yi kira ga magoya bayan jam’iyyar a jihar Kaduna da su lakadawa duk wanda ya zabi wata jam’iyya da ba jam’iyyar PDP ba dukan tsiya sannan su tabbata sun kwana da shirin ko ta kwana a jihar.
Ben Bako ya bayyana haka ne a taron kamfen din jam’iyyar a garin Kafanchan.
A bidiyon da muka gani, Bako ya kara da cewa duk wanda ya tare su a hanya a lokacin da suke dakon kuri’u daga kauyukan su su tabbata sun jide da kya sannan su yi ta haka har sai sun iso garin Kafanchan inda za a tattara kuri’u.
” Mun ji an ce wai za a kawo sojoji wannan yankin a lokacin zabe. Abin da nake so in tambaye ku an kawo sojoji a yankin a lokacin da ake kashe mu.? jama’a suka ce a’a. Haka ya ci gaba da ingiza mutanen da suka halarci filin taron da muggan kalaman da kalaman batanci da za su iya tada zaune tsaye a lokacin Zabe jama’a kuma suna kowa suna lallai za su tabbata sun shirya yin fito-na-fito da jami’an tsaro da duk wanda ya zabi wata jam’iyya da ba PDP ba a yankin kudancin Kaduna din.
Idan ba a manta ba a irin haka ne gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai shima ya zaro wasu kalamai inda yake cewa duk wanda ya saka wa Najeriya baki a harkokin zaben ta za a koma gida da gawar sa. Wannan magana ya tada wa mutane da dama hankali da har sai da gwamna El-Rufai ya fito ya wanke kansa, Cewa ba abinda yake nufi ba kenan.
Sai dai kuma shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa lallai zai tabbata ba a tada yamutsi a lokacin zabe ba, yana mai cewa burin sa shine ayi zabe lafiya.
[youtube https://www.youtube.com/watch?v=ClxGaKwT8Ys&w=560&h=315]
Discussion about this post