Duk wanda ya tona asirin masu sayen kuri’a za mu biya shi lada – EFCC

0

Hukumar EFCC ta bayyana albishir cewa za ta biya lada ga duk wanda ya fallasa masu sayen kuri’u a zabe mai zuwa da za a fara jibi.

Kakakin Yada Labarai na EFCC, Tony Orilade ne ya fitar da wannan sanarwa jiya Laraba a Abuja. Ya ce wannan tsari ya na daga cikin tsarin busa usur din fallasa masu harkallar kudade da EFCC ta shigo da shi.

Orilade ya ce Shugaban EFCC, Ibrahim Magu, ya gargadi duk mai saye da mai saidawa cewa su kuka da kan su, domin idan an kama su, to hukunci zai hau kan su.

Magu ya ce a cikin dokar zabe ta 2010, akwai sashe na 124 wanda ya ce hukuncin tara ta naira 500,000 ta hau kan wanda aka kama ya na sayen kuri’u da shi ma mai sayarwar.

Ya ce akwai karin dauri na watanni 12 ko mutum ya biya tara, ko kuma a hada masa biyu din duka.

“Sannan kuma ba zai kara yin zabe ba, har sai bayan ya biya tarar tukunna.

Magu ya ce sun samu bayanin cewa akwai wasu ‘yan siyasa da su ka yi kokarin shigo da kudade daga waje domin su rika sayen kuri’u. Ya ce sun toshe hanyar da za su iya shigo da kudaden.

Daga nan sai ya yi kiran cewa kada a yi nauyin kafa, da an ga masu dillancin sayen kuri’u, to a gaggauta sanar da EFCC.

Share.

game da Author