Duk wanda ya saka mana baki a zabe, za a koma da gawar sa ne gida – Inji El-Rufai

0

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana cewa Najeriya ba za ta zuba ido ta bari wani daga kasan waje ya zo kasarnan ya saka mata baki a harkokin ta ba musamman a wannan lokaci na zabe cewa duk wanda yayi haka toh lallai ko za a koma da gawar sa ne gida.

Ya yi wannan kasassaba ce kwanaki kadan bayan da wasu kasashen Turai da Amurka suka nuna damuwar su a akan yadda gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta dakatar da Cif Jojin Najeriya Walter Onnoghen ana saura wata daya kacal a yi zabe.

Zaben wanda za a yi a ranakun 16 Ga Fabrairu da 2 Ga Maris, zai samu halartar kungiyoyin sa-ido daga kasashen waje har 28.

Daga cikin su tuni har Kungiyar Tarayyar Turai ta turo tawagar mutane 40, ita kuma Kungiyar Kasashe Rainon Ingila ta turo tawagar mutane 20, a karkashin tsohon shugaban kasar Tanzania.

Gwamna El-Rufai, wanda dan jam’iyyar APC ne mai mulki, ya na a sahun gaban masu goyon bayan Buhari na karshe, ya caccaki jam’iyyun adawa da kungiyoyin kasa da kasa masu sa-ido kan zabe.

Ya yi caccakar ce a wata hira da aka yi da shi a gidan talbijin na NTA a jiya Talata da dare, a wani shiri mai suna ‘Tuesday Live’. Cyril Stober ne ya tattauna da shi.

“Masu kiran wasu su shigo su sa-baki cikin harkokin Najerya, to a fada musu mu na jiran mu ga duk wanda zai shigo ya yi mana katsalandan. Wanda ya kuskura ya shigo, to sai dai a maida gawarwakin su a cikin buhunan daukar gawarwaki can a kasashen da suka fito.”

Ya ce shiga harkokin zaben da Najeriya ta yi a Saliyo da Laberiya, ai ta yi ne saboda amincewar kungiyoyin kasashe da kuma hakkin makwabtaka da ke tsakanin kasashen da Najerya.

Ya ce Najeriya kasa ce mai ‘yancin kanta, don haka ba za ta taba amincewa ta bayar da kai ga wasu kasashen waje ba.

“ Mu na ta kokarin mu ga mun tafiyar da kasar mu a tsanake gwargwadon iyawar mu.

Dama kuma kakakin yada labarai na fadar shugaban kasa fada kwanan baya cewa Najeriya ba ta za yi kasa a guiwa ba wajen daura yaki da duk kasar da ta yi mata katsalandan a sha’anin ta na cikin gida.

Ya yi wannan furucin ne a bisa martani ga korafin da wasu kasashe suka yi dangane da dakatar da Cif Jojin Najeriya da Buhari yayi.

Kakakin yada labarai na El-Rufai bai amsa kiran da aka yi masa ba. Haka shi ma Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed wanda ya ke ta watsa farfagandar yaki da kalaman batanci, bai ce komai ba har yanzu.

Cikin 2017, gwamnatin Buhari ta aika da sojoji wajen kawar da Yaya Jammeh daga mulki a kasar Gambiya.

Tuni masu sharhi su na ta la’antar wannan furuci da El-Rufai yayi a daidai gabatowar zabe.

Share.

game da Author