Duk Wanda ya sace akwatin Zabe zai iya kwanan makabarta ranar- Inji Buhari

0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargadi masu shirin tada rikici da sace akwatunan Zabe da su canja shawara domin duk Wanda aka Kama yana kokarin yin haka zai iya rasa ransa.

Buhari ya yi wannan gargadi ne a wajen taron jiga-jigan Jam’iyyar APC da ya gudana a garin Abuja.

Buhari ya Kara da cewa bai ji dadin dage Zabe da hukumar INEC ta yi zuwa mako na gaba ba yana mai cewa shugaban hukumar ya nuna gazawar sa matuka Kuma ya bashi kunya.

Duk a wajen wannan taro Shugaban Jam’iyyar APC Adams Oshiomhole, ya yi kiran da a yi wa jami’an Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC garambawul.

Ya yi wannan kiran ne a yau a wurin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC, wanda suka gudanar a yau Litinin a Abuja, wanda cikin mahalarta har da Shugaba Muhammadu Buhari, wanda shi ne dan takarar shugabancin kasa a zabe mai zuwa.

Shi ma Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya halarci taron.

Oshiomhole ya yi zargin cewa akwai wasu Kwamishinonin Zabe da ke wa jam’iyyar PDP aiki.

Ya fito gaba-gadi ya ambaci sunan Kwamishinan Zabe na Jihar Akwa Ibom, Mike Igini.

Idan ba a manta ba, shi kuma Mike Igini ya tara manema labarai ya yi musu korafin cewa wasu batagarin ‘yan siyasa na neman dagula harkar zabe.

Ya yi wannan kakkausan kalamin ne bayan da hargitsin da ya tashi a lokacin da aka tattara motocin daukar kayan zabe a jihar Akwa Ibom, aka yi yamutsin da har aka kona motoci 13.

Igini dai bai ambaci ko wace jam’iyya ce batagarin ‘yan siyasar su ke ba.

PREMIUM TIMES ta kawo muku labarin banka wa motocin 13 wuta a Jihar Akwa Ibon tun a labaran da ku ka karanta a ranar Asabar.

“Abin takaici ne a ce ‘yan siyasa wadanda su ne ke fin kowa cin moriyar dimokradiyya, ya kasance kuma su ne a sahun gaba wajen neman kawo mata barazana.” Haka Igini ya furta a ranar Asabar.

Share.

game da Author