Gwamnan jihar Kaduna ya bayyana cewa duk wanda ya karyata kisan kiyashin da aka yi wa mutanen Kauykan karamar Kajuru wannan mutum ya zauce, yana neman a duba shi.
El-Rufai ya yi karin haske game da ainihin yawan mutanen da suka rasa rayukan su a wannan hari bayan taro da ya halarta da shugaban kasa a fadar gwamnati dake Abuja.
” Bari in gaya muku cewa zuwa yanzu ma mutanen da aka kashe sun kai 130 a lissafin da muka yi zuwa yau.
Idan ba a manta ba a ranar Juma’a ne gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da kisan mutane 66 a karamar hukumar Kajuru.
Akalla yara 22 da mata 11 ne aka yi wa kisan gilla a wannan hari da aka kai.
El-Rufai ya ce dalilin da ya sa aka dan jinkirta fadin yawan mutanen da suka salwanta a harin shine don ana tattara yawan su ne, sannan kuma za a fidda sunayen wadanda aka kashe a wannan hari.
Discussion about this post