Duk wanda ya fito zanga-zanga a Kaduna, zai yabawa aya zaki – Inji Kwamishinan ‘Yan sandar jihar

0

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna Ahmad Abdurrahman ya gargadi mutanen jihar da duk wata kungiya da ke shirin fitow yin zabga-zanga a jihar da ya kwana da shirin cewa jami’an tsaro ba za su zuba masa ido ba.

Abdulrrahman ya ce dokar hana zanga-zanga a jihar Kaduna na nan daram dam, saboda haka duk wani mai shirin yin haka ya kwana da shiri domin jami’an tsaro ba za su barshi ba.

Akwai rade-radin cewa wasu kungiyoyi na shirin fitowa domin yin zanga-zanga a jihar ranar Litinin.

Sai dai kuma kwamishina Abdurrahman bai fadi ko wani irin zanga-zanga bane za ayi a jihar da yake yin irin wannan shela.

” Bamu san ko wani irin zaga-zanga suke shirya wa amma dai su sani cewa, a wanan jiha ta Kaduna, akwai dokar hana zanga-zanga kuma tana nan tana aiki. Duk wanda ya fito don haka zai dandana kudar sa.”

Share.

game da Author