Duk Wanda ba shi da Katin Zabe, bashi ba Zabe – Inji Hukumar Zabe

0

Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) Mahmood Yakubu ya jadadda cewa idan fa mutum bashi da ainihin katin zabe ko kuma na’uran tanttance katin zabe ya kasa tattance katin sa to fa mutum ba zai iya kada kuri’a ba.

Yakubu ya sanar da haka ne ranar Juma’a a wata zama da hukumar ta yi a Abuja tare da masu sa ido a zabe na ciki da wajen kasa da jami’an tsaro domin bayyana shirin zabe da hukumar ta yi.

Ya kuma kara da cewa masu zabe za su iya zuwa rufunar zabe da wayar su na hannu amma za a hana waya idan lokacin jefa kuri’a ya yi.

Ya ce haka zai taimaka wajen hana siyan kuri’un mutane.

Idan ba a manta ba a jiya Alhamis ne INEC, ta ce ya zuwa ranar rufe karbar katin zabe, ‘yan Najeriya miliyan 72,775,565 ne suka karbi katin zaben su a hannu.

Hakan ya yi nuni da cewa jimillar kuri’un da za a jefa a ranar Asabar mai zuwa ba za su wuce miliyan 72,775,585 ba kenan.

Domin babu wanda za a amince ya jefa kuri’a sai wanda ya yanki katin rajistar yin zabe.

Sannan kuma INEC ta ce yawan katin zabe da ba a karba ba, sun kai miliyan 11,228,582.

Hakan kuma na nuni da cewa duk wanda ya yi rajista amma bai je ya karbi katin sa ba, to ba za a bari ya yi zabe ba, ko ma wane ne.
Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana cewa mutane milyan 84 ke da rajitar zabe a hannun su.

INEC ta yi alkawarin buga adadin yawan katin zaben da ba a karba ba har yanzu.

Tun a ranar 11 Ga Fabrairu ne INEC ta rufe kofar karbar katin zabe ga wanda bai karba ba tun tuni.

Ya ce dukkan katin zaben da ba a karba ba, an adana su a Babban Bankin Najeriya, CBN, sai bayan an kammala zabe sannan INEC za ta karbo su ta ci gaba da raba wa masu su.

Share.

game da Author