Dino Melaye ya fara nasara daga sama har kasa

0

Jam’iyyar PDP ce ta yi nesa da rinjaye mai yawa a Mazabar Orekere-Amuro, cikin Karamar Hukumar Mopamuro, a Jihar Kogi.

A sakamakon zaben da Jami’in Tattara Kuri’u ya bayyana a jiya da dare, Ojebodeh ya bayyana sakamakon na Mazabar Ward 6 ne a makarantar YLGEA jiya Asabar da dare.

A zaben shugaban kasa PDP ta samu 760, APC 447.

A zaben majalisar dattawa PDP ta samu 690, APC kuma 447.

Dino Melaye ya na kafsa takara ne da Smart Adeyemi na jam’iyyar APC.

Smart Adeyemi ne ke kan kujerar sanatan shiyyar a karkashin PDP, amma Dino ya kayar da shi a zaben 2015 a karkashin APC.

Rigingimun siyasa suka sa Adeyemi ya koma APC daga PDP, shi kuma Dino ya koma PDP daga APC.

Rahotanni daga Daily Trust kuma sun nuna Dino ya lashe sauran rumfunan da suka rage, inda ya yi gabala a dukkan zabukan uku.

Share.

game da Author