Dino Melaye na kan gaba a zaben kujeran sanatan Kogi ta Yamma

0

Sanata Dino Melaye ya yi wa abokin takarar sa Smart Adeyemi ratan gaske a sakamakon zaben kujerar Sanatan Kogi ta Yamma.

Sanata Dino na jam’iyyar PDP ya lashe zaben duka kananan hukumomi hudu da ka riga aka bayyana sakamakon su cikin kananan hukumomi bakwai da suke wannan shiyya.

Ga yadda sakamakon yake kamar yadda aka bayyana a garin Lokoja.

Karamar Hukumar Lokoja Dino nada Kuri’u 24,576, Smart 18, 800, Yagba West Dino ya samu kuri’u 8, 942, Smart kuma 6,799.

A karamar hukumar Mopa-Muro Dino ya samu kuri’u 5,112, Smart kuma 3, 658.

Haka kuma a karamar hukumar Yagba East Dino ya samu kuri’u 8, 638 shi kuma Smart 5, 077.

Yanzu saura kananan hukumomin Ijumu, Kabba/Bunu da Kogi.

Share.

game da Author