Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya fatattaki kwamishinan yada labaran sa Barrister Bello Goronyo.
Bello Goronyo ya bayyana ficewar sa daga jam’iyyar PDP bayan a taron gangamin jam’iyyar APC da tsohon gwamna Aliyu Wamakko ya jagoranta a garin Sokoto ranar Talata.
Bello shine kwamishinan yada Labaran gwamnatin Jihar Sokoto sannan shine darektan Kamfen din PDP a Jihar.
Darektan Yada labaran gwamna Tambuwal, Abubakar Shekara da shine ya you shelan koran kwamishinan da gwamna Tambuwal yayi ya Kara da cewa tuni har gwamnan Jihar ya umarci babban sakataren ma’aikatan yada Labarai ya ci gaba da rike ma’aikatan.
” Wanna mataki da gwamnati ta dauka na koran kwamishina Bello Goronyo ya zama dole ganin cewa an gano yana yi wa ayyukan ci gaba da gwamna Tambuwal yake yi a Jihar zagon Kasa.