Ta tabbata cewa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta dage zaben Shugaban Kasa da za a gudanar yau Asabar da shi da na Majalisar Dattawa, zuwa ranar 23 Ga Fabrairu.
Yakubu ya kara da cewa shi kuma zaben gwamna, na majalisar jihohi da na kananan hukumomin Abuja FCT, za a gudanar da su ne a ranar 9 Ga Maris.
Sanarwar haka ta fito ne daga bakin Shugaban Hukumar, Farfesa Mahmood Yaukubu, a cikin tsakar dare a hedikwatar INEC, ana saura sa’o’I kadan kafin a fara shirin fita aikin jefa kuri’a.
Dama kafin wannan sanarwa, sai da PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa za a dage zaben saboda wasu dalilai na rashin isar kayan zabe a wasu jigohi da wuri.
Daga cikin jihohin da PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa ba a kai kayan zabe ba, har da jihar Neja da Ekiti.
PREMIUM TIMES ta shaida a lokacin cewa Kwamishinonin INEC na can sun a taron gaggawa a hedikwatar hukumar, kuma wata majiya daga cikin su ta shaida cewa babu makawa sai an dage zaben.
Amma dai a lokacin majiyar ta ce ba ta san ko kwana daya za a kara ba ko kuma sati daya.
Yakubu ya yi wannan sanarwa ce da karfe 2:30 daidai.
Shugaban na INEC ya yi karin haske da cewa a yau Asabar zai yi karin hasken cikakken dalilin dage zaben da sati daya.
“Biyo bayan bin diddigi na yin nazarin tsare-tsaren da INEC ta yi da kuma irin yanayin yadda shirin na ta ke tafiya har zuwa yanzu, da kuma dalilan alkawarin da INEC din ta dauka cewa za ta gudanar da sahihin zabe kuma karbabbe, wannan hukuma ta cimma matsaya cewa gudanar da zabe a ranar Asabar ba zai yiwu ba.
“Dalilin haka INEC ta dage zaben Shugaban Kasa da na Majalisar Dattawa zuwa ranar 23 Ga Fabrairu, shi kuma na Gwamna da na Majalisar Jiha da na Kananan Hukumomin FCT zuwa ranar 9 Ga Maris, 2019.”
“Wannan ne zai sake ba INEC damar shawo kai da magance dukkan kalubalen da aka fuskanta, domin a kara inganta matakan gudanar da zaben. Wannan mataki ne mai tsaurin gaske, amma fa daukar sa ya zama wajibi domin a tabbatar da an gudanar da zabe cikin nasara, yadda zai kara wa dimokradiyyar mu armashi.
Daga nan sai Yakubu ya ce zai gana da dukkan masu ruwa da tsaki a harkar zabe a yau Asabar a Cibiyar Gudanar da Taro ta Kasa da Kasa, domin yin cikakken jawabi.
Za a gudanar da taron ne karfe 2 na rana a yau Asabar.
Matsaloli da aka samu a jihohin Neja da Ekiti
Wasu daga cikin jihohin da ba kayan zabe ba su isar musu ba, har da jihar Ekiti da Neja.
A Jihar Neja dai an ruwaito Kwamishinan Zabe ya ce kuri’un shiyyar sanata biyu daga cikin sanatoci uku na jihar, duk sun salwanta ya zuwa ranar Juma’a da dare.
Can a Jihar Ekiti kuwa, tsohon gwamna Ayo Fayose, ya zargi INEC da laifin boye kayan zabe da gangan a wasu jihohi da nufin dagula wa PDP lissafi.
Fayose ya kara da cewa cewa har zuwa ranar Juma’a 9 na dare, ba a kai takardun da ake rattaba adadin kuri’un da kowane dan takarar shugaban kasa, na Majalisar tarayya da na Majalisar Jiha ya samu a a Jihar Ekiti ba.
Kakakin Fayose, Lere Olayinka ya ce jihohin da ke fuskantar wannan matsalar sun hada a Ekiti, OyoTaraba, Edo, Niger, Ogun, Rivers da ma wasu jihohi.
Tuni dai manyan Jam’iyyu biyu da APC mai mulki da PDP babbar mai adawa suka rika jifar junan sau da cewa kowace ita ce ta haifar da wannan jinkiri domin ta shirya magudi.
Shi kan sa dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar, APC ya zarga da laifin hada baki su yi magudi.
Akwai cikakkun wadannan labarai na zarge-zarge duk PREMIUM TIMES ta kawo muku.