Dalibai Miliyan 1.8 ne suka yi rajistar rubuta jarabawar JAMB a 2019

0

Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’o’in Kasar nan (JAMB) ta bayyana cewa a 2019 dalibai miliyan 1.8 ne suka yi rajistar rubuta jarabawar.

Darektan yada labarai na hukumar Fabian Benjamin ya sanar da haka da yake ganawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Alhamis a a garin Legas.

Benjamin ya ce hukumar ta rufe yin rajista da siyan fom tun a ranar 21 ga watan Fabrairu.

Ya ce amma wadanda suka sayi fom din su kafin ranar 21 ga watan Fabrairu za su iya yin rajistan jarabawar daga lokacin zuwa karfe 12 na daren ranar 25 ga watan Fabrairu.

Benjamin ya kuma karyata rade radin da wasu ke yada wa cewa wai an fara buga takardar shiga rubuta jarabawar.

Ya ce wannan batu karya ce domin babu yadda za a iya buga wannan takardar ba tare da hukumar ta tsayar da ranar rubuta jarabawa ba.

” Akan fara buga wannan takardan ne mako biyu kafin ranar jarabawar.

Ya yi kira ga mutane da su kwantar da hankalin su cewa nan ba da dadewa ba hukumar za ta sanar da ranar rubuta jarabawar.

Share.

game da Author