Dahiru Bauchi ya yi tir da Musulmai masu zagin Musulmai a kan siyasa

0

Fitaccen malamin addinin Musulunci kuma jagoran mabiya Darikar Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Bauchi, ya yi tir da babi’un wasu malaman addini da ke tsine wa musulmai a kan bambancin siyasa.

Bauchi ya nuna rashin jin dadin sa a lokacin da Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara ya kai masa ziyara a gidan sa.

Malamin ya shaida wa mabiyan sa zaman lafiya da sauran al’umma da ake zaune tare, musamman wadanda ba addinin su daya ba.

Ya kuma yi kira da a kara yin nesa da ra’ayin rikau da kullatar juna.

“Da a zabi dan Izala wanda bai ganin girman dan Tijjaniya kuma bai yarda da cewa dan Tijjaniya musulmi ba ne, to har gara a zabi Kirista.” Inji Dahiru Bauchi.

“Da Izala da Darika duk suna karkashin tutar musulunci ne, shi ne addinin mu. Amma shi mutumin da malaman Izala din ke ta kokarin tirsasa mana, an san shi wajen muzanta manyan malaman mu. Amma kuma ya na kiran kan su Musulmi.

“Wannan ai kamar ka zagi mahaifi na, mahaifiya ta, malamai na da shehunai na ne. To mu ba za mu taba goyon bayan wannan mutumin ba.”

Yayin da ya yi kira ga al’ummar Bauchi su guji siyasar raba kan mabiya addinai, jagoran na Tijjaniya ya kuma yi kira ga al’ummar mazabar Bogoro/Dass/Tafawa Balewa su sake zaben Dogara, saboda gagarimin ciyar da mazabar sa da ya yi.

Dahiru yace kowa ya shaida yadda Dogara ke siyasar ciyar da jama’a da kuma mazabar sa tare da rashin cusa addinanci a zukatan siyasar jama’a.

Da ya ke jawabin godiya, Dogara ya gode da irin addu’ar da Sheikh Dahiru Bauchi ya yi masa.

Share.

game da Author