Dage zabe zai ba Hukumar Zabe damar yin shiri da kyau – Minista Shittu

0

Ministan sadarwa Adebayo Shittu ya bayyana cewa dage zaben da hukumar zabe mai zaman kanta ta you (INEC) zai samar wa hukumar damar yin shirin da ya kamata wajen ganin zaben ya gudana yadda ya kamata.

Shittu ya fadi haka ne da yake zantawa da manema labarai ranar Asabar a jihar Oyo.

Ya ce duk da cewa hukumar bata bada kwararan dalilan da ya sa ta dage zaben ba amma hakan ba shine farau ba a kasarnan.

Shittu yace a nasa ganin dage zaben zai taimaka wa jam’iyyar APC wajen toshe ramukan da bata gama toshewa ba a baya kafin sabbin ranakun zaben.

Ya kuma yi kira ga mutane da kada su bari wani ya ruda su da kudi wai don su Zabe shi.

Mataimakin kakakin majalisar dokoki na jihar Musah Abdulwasi ya nuna rashin Jin dadin sa game da dage zaben da aka yi sannan yayi kira ga Hukumar Zabe da ta yi amfani da wannan da dama wajen inganta shirinta.

Idan ba a manta ba a yau Asabar ne da misalin karfe 2 na safe INEC ta sanar da dage zaben shugaban kasa da na majalisar Tarayya da za ati a fadin kasar nan a ranar Asabar din.

Shugaban hukumar Mahamood Yakubu ya sanar da haka a hedikwatar hukumar dake Abuja inda ya kara da cewa hakan ya zama dole saboda matsalolin da hukumar ta samu na rashin kai kayan zabe a wasu jihohin dake kasar nan da wuri da kuma wasu matsaloli da ya sha mata Kai.

INEC ta daga zaben shugaban kasa da majalisar majalisar kasa zuwa ranar 23 ga watan Fabrairu sannan zaben gwamna ranar 9 ga watan Maris.

Share.

game da Author