Idan ba a manta ba a ranar Asaba 16 ga watan Fabrairu ne Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta sanar da dage zabe da za ayi a ranar zuwa mako mai zuwa.
Abin bai yi wa mutanen Najeriya dadi ba saboda ko wasu da dama sun tafi jihohin su domin kada kuri’a. Wasu ko aurarraki ne za ayi amma kuma dole aka daga domin haka.
Kamfanoni, gidajen jaridu, jami’an tsaro da dai sauran su duk sun afka cikin rubibi bayan makudan kudade da suka riga suka kashe wajen shirye-shirye a dalilin wannan zabe.
PREMIUM TIMES HAUSA ta nemi ji daga bakin masu karatu domin su tofa albarkacin bakin su game da wannan abu da ya faru.
Hassan M. Ringim Gaskiya ba mu ji dadin haka ba. Abin da muke tsammani shine, idan an aikata kuskure jiya, to ya kamata a yi nazari da aiki tukuru don ganin bai maimaitu a karo na uku ba.
Akwai wata bukata akan wannan lamari. Muna fatan mutane za su fahimci halin da Najeriya take ciki.
Jamilu Usman Dakata Gaskiya irin wannan yanasa masu kada kuri’a sugaza wajan fita kada kuri’arsu Agaba saboda rashin sanarwa da wuri, fatammu Allah yasa hakan yazama alkairi.
Nauwas Haruna BJ aslm premium times agaskiya dage zabenda hukumar zabe ta kasa tayi inec hakan yakarawa jaddadawa Yan Nigeria cewa ba,a shirye sukeba donyin zaben gaskiya hakan Kuma zai kasance musu abun kunya a idon duniya gabaki daya. ammana fatanmu anan shine Allah yasa a gudanar da zaben cikin gaskiya da adalci don a bawa talakawa abunda suka zaba
Aminu Abdu Bakanoma Sanimainagge Dagewar bata yimana dadi ba kasancewar mutane dadama suntsayar da ayyukansu sunbaro inda suke sanaoinsu Amma kwatsam a dage zabe a gajeran lokaci hakan baiyimana kyauba.
Abubakar Ashiru Abubakar Da farko dai Allah ya isa, kuma wlh bazan yafeba. Nabiyu duk wlh Mun zalinci Jonathan idan mukace babu komai akan daga wannan zaben. Tarihi dai rai gareshi kuma wlh tarihi zai iya maimata kansa. An cucemu an bata mana lokaci Allah ya isa wlh.
Ibrahim Idris Dage zabe ba sabon abu bane a wannan kasan tamu, idan hukuman zabe ta ga ba ta shirya ba tsaf domin gudanar da zaben ba, toh ya kama dole a dage ta har zuwa lokacin da zasu shirya domin gudanar da sahihiyar zabe. Fatan mu Allah ya zaba mana mafi alkhairi
Danjuma Abdul-jabbar Kamil Inda nine shugaban hukumar zabe da sai nayi murabus daga matsayina. Sakamakon gaza gudanar da zabe da nayi a lokachin da aka tsara za’a aiwatar. Koba komi zan tsira dafa zargin masu kallona da mai shirin aiwatar da magudi da al’mun dahana. Sannan na tsira da mutunchina da darajata a idanun kasata Nigeria da dunia baki daya.
Al-ameen Adam Wannan rashin adalci ne na Buhari da jam’iyar APC saboda sun hango faduwa gadan-gadan, amma ba komai mudai munsan shure-shure ba ta hana mutuwa, mune dai masu zabe kuma muna nan har sati mai zuwa Insha Allahu, kuma su sani wannan karin nasara ga jam’iyar PDP.
Hussyne Mansour Ahmed A gaskiya Dage zabe da hukumar zabe tayi baiyi mana dadi ba kuma bai kamata ba. Saboda banga dalilin dazai sa a dage zabe ba. INEC ta dade tana shirye shirye game da zaben nan sama da shekaru uku, kuma sun samu makudan kudade daga gwamnatin tarayya domin gudanar da zaben. Mutane dayawa sunyi tafiya daga gurare daban daban wasu har daga kasashen ketare domin su kada Kuri’a, bayan sun kashe kudadansu da kuma wahala da suka sha amma ace an dage zabe. Abin mamaki shine har zuwa ranar Jumma’a Shugaban hukumar zabe yace a shirye suke kuma sun kammala dukkan shirye shiryensu na gudanar da zabe. Amma sai gashi “in less than 7 hours “ kusan karfe 2am na dare ace an dage zabe alhalin mutane dayawa wasu sunyi barci a lokacin da aka fitar da wannan sanarwar.
Dage zaben nan ya nuna cewa hukumar zabe basu shirya ba, kuma ya nuna cewa Professor Yakubu shugaban hukumar zaben baisan aikinsa ba. Kuma dage zaben nan ya jayo mutane dayawa sun daina ganin kimar hukumar zaben. Kuma ya ragewa Nigeria daraja a idon duniya baki daya. Kuma yanxu duk wanda ya fadi wannan zaben, yana da hujjar dazai iya zuwa kotu yace dage zaben da akayi anyishi ne da wani manufar magudin zabe.
Allah yasa haka shine mafi alkyri. Allah yasa ayi zabe lafiya a gama lafiya. Ameen.
Algarqawiy Kmashi Abin kunya sai a kasata Nigeria awancen karan 2015 da Inec ta daga zabe sai akace laifin gwamnati ne,amma yanzu sabi da rashin adalci da kuma son buhari sai akace laifin Inec ne,har jam’iya mai mulki tayi tur da Inec.Ya Allah ka ganar da yan Nigeria daga wannan duhun son
Abdul Maliki Sokoto, Tukur Adamu, Mohammed Nazifi, Anas Sanusi,Bashir Zubairu Gwammaja, Ghali Imran, Armayau Hamisu, Abubakar Abdullahi, Abdallah Awwal Yardaje da wasu da dama addu’a suka yi Allah ya sa haka shine yafi zama Alkhairi ga ‘yan Najeriya.
Shiko Abdulkareem Ak Zakari cewa yayi, ” Hakan na nuna cewar gwabnatin Buhari Bata shirya sauka daga Kan mulki ba a 29 may 2019″
Wasu kuma kamar Ismail Namadi cewa ya yi, Kawai kulle kullene na gwamnatin zalunchi ta buhari gamida hada gwiwa da inec domin ganin anyiwa jamiyyar adawa ta PDP magudi. Toh munaso su sani wallahi mu sai Atiku.
Discussion about this post