DAGE ZABE: INEC ta jahilci dokar hana kamfen, mu dai za mu ci gaba -PDP

0

Jam’iyyar PDP ta ce ta yi shiri tsaf domin sake ci gaba da kamfen, duk kuwa da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce kada a ci gaba da zabe.

PREMIUM TIMES ta ruwaito labarin dage zabe zuwa ranar 2 Ga Fabrairu, 2019, inda kuma Shugaban Hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ya yi sanarwar cewa dage zabe ba ya na nufin jam’iyyu za su ci gaba da yakin neman zafe ba ne.

Dokar zabe ta ce za a daina kamfen ne ana saura kwana daya a yi zabe.

A bisa wannan dalili ne PDP ta ce tunda an dage zabe zuwa mako daya, to za ta ci gaba da kamfen har nan da ranar Alhamis mai zuwa, ana gobe zabe kenan.

Sakataren Yada Labarai na Kasa na PDP, Kola Ologbondiyan ne ya furta wannan sanarwa a jiya Lahadi da yamma a Abuja.

Ya ce jam’iyyar PDP ta yi fatali da wannan sanarwa ta hana kamfen cikin ranakun da INEC ta kara zaben, ya na mai cewa kuskure INEC ta yi.

Ya ce shugaban INEC bai kawo wani gamsasshen bayani daga doka ba wanda ya nuna cewa tabbas an hana kamfen a cikin kwanakin da aka dage zabe.

“Mu dai mun tsaya a kan abin da dokar zabe ta 99 (1) ta gindaya cewa a dakatar da kamfen ana saura awoyi 24 kafin zabe.”

“Don haka tunda an dage zabe ba a gudanar da shi a ranar 16 Ga Fabrairu ba, sai aka kara mako daya, to za a ci gaba da kamfen sai tsakar daren 2i Ga Fabrairu za a dakata.”

Shi ma shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshimhole ya yi wannan barazana cewa APC za ta ci gaba da kamfen tunda an kara wa’adin lokacin zabe.

Share.

game da Author