DAGE ZABE: INEC ta dawo da kayan zabe da aka rarraba a fadin kasar nan

0

Domin tabbatar da inganci da sahihancin zaben shugaban kasa da na majalisar dattawa, wanda za a gudanar ranar Asabar mai zuwa, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana cewa ta dawo da kayayyakin zaben da ta rigaya ta fara tuttutawa a cikin mafi yawan jihohin kasar nan.

An rarraba kayan ne domin gudanar da zaben da za a yi a ranar 16 Ga Fabrairu da ya gabata, wanda sa’o’i kadan kafin fara zabe, sai Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya bada sanarwar dagr zaben.

PREMIUM TIMES ta bada labarin kalubalen da shugaban na INEC ya ce an fuskanta, wadanda tilas su ka sa aka dage zaben zuwa ranakun 23 Ga Fabrauru da kuma 2 Ga Maris.

Kungiyoyin rajin kare dimokradiyya irin su CDD, sun nuna tsananin damuwa ganin cewa yawancin kayan zaben duk an rigaya an tura su jihohi da kananan hukumomi kafin a soke zaben.

A kan haka ne INEC ta fara dawo da kayan zaben da aka rigaya a ka raba. Cikin jihohin da aka maida na su din akwai Lagos, Anambra, Enugu da Filato.

JIHAR LAGOS

INEC ta ce ta kammala sake tattara dukkan kayan zaben da aka rigaya aka rarraba a ilahirin kananan hukumomi 20 da ke cikin jihar.

Kakakin INEC na jihar Lagos, Femi Akinbiyi, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai, NAN cewa an kammala tattara su, an dawo da su, kuma duk an kimshe su a Babban Bankin Tarayya reshen jihar dominn adanawa da kuma kulawar jami’an tsaro.

Ya ce har da Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar da kan sa ya yi aikin sa-idon dawo da kayan daga wasu kananan hukumomin da ya sa-ido da kan sa.

ANAMBRA

Shi ma Shugaban Wayar da Kai da Kuma Yada Labarai na INEC a Jihar Anambra, Leo Nkedife, ya ce an dawo da dukkan kayan zaben INEC ta raba a jihar.

Ya shaida wa manema labarai haka a Awka jiya Lahadi cewa hakan zai bada cikakkiyar damar jami’an tsaro su rika kula da su har zuwa ranar da za a sake rarraba su domin zabe mai zuwa na ranar Asabar.

Ya ce su na can duk an killace su a Babban Bankin Najeriya, reshen Jihar Anambra.

FILATO

A Jihar Filato ma, Jami’in wayar da kai da yada labarai na INEC, Osaretin Imahireogbo, ya ce an dawo da dukkan kayan zaben da aka rigaya aka raba a fadin kananan hukumomi 17 da ke jihar.

Shi ma ya ce an killace su a Babban Bankin Najeriya reshen Jihar Filato domin jami’an tsaro su ci gaba da kula da su.

Share.

game da Author