DAGE ZABE: Atiku ya zargi Buhari da tauye wa ‘yan Najeriya damar su

0

Jim kadan bayan sanarwar da INEC ta bayar cikin dare na dage Zabe, sai dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya zargi Shugaba Muhammadu Buhari da kokarin tauye wa ‘yan Najeriya damar su ta yin zabe.

Sai dai kuma Atiku ya yi kira ga daukacin ‘yan Najeriya su dauki hakuri da juriya, kada su bari a harzuka su kafin a kai ga sabbin ranakun da za a gudanar da zaben.

Atiku ya yi wannan kalami ne jim kadan bayan da INEC ta bayyana wata ranar da za ta gudanar da zabe.

Sai dai kuma Shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa za a yin zaben a ranakun 23 Ga Fabrairu da kuma 9 Ga Maris, 2019.

An dage zaben ne ana saura sa’o’i shida a fara fita jefa kuri’a.

Dimbin ‘yan Najeriya ba su ji dadin yadda aka dage zaben ba, musamman ganin yadda suka rika yin Allah wadai da dage zaben a soshiyal midiya.

Jawabin Atiku ya biyo bayan jawabi da Ofishin Kamfen a Buhari ya fitar, wanda ya zargi jam’iyyar PDP da laifin haddasa dage taro, kuma ya roki ‘yan Najeriya su goya wa INEC baya, ganin yadda INEC din ta ki yarda ta yi wa PDP abin da ta ke so. Wannan dai zargi ne da Ofishin Kamfen na Buhari ya yi.

“Kawai dai Buhari ya na so ne ya tauye wa ‘yan Najeriya damar da suke da ita ta yin zabe, domin dage zaben zai haifar da raguwar masu jefa kuri’a a ranakun da aka sake aza cewa za a yi zaben. Don haka ina kira ga ‘yan Najeriya kada su yi fushi, su kara garzayawa wurin jefa kuri’a fiye ma da niyyar su ta yau. A ranar 23 Ga Fabrairu da 9 Ga Maris, kowa ya je ya yi zabe.”

Share.

game da Author