Da zarar na dare kujerar mulki zan fara shirin sake fasalin Najeriya – Inji Atiku

0

Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa idan ya samu nasarar lashe zaben 2019, to da wuri zai fara shirin sake fasalin Najeriya.

Atiku ya fadi haka ne a wurin yakin neman zabe a garin Fatakwal, babban birnin jihar Ribas. Ya ce idan ana so a samu gagarimin ci gaba to a sauya fasalin kasar nan.

Ya ce zai sake fasalin Yankin Neja Delta da kuma sauran dukkan shiyyoyin kasar nan bai daya.

Dan takarar ya nuna irin ko-in-kula da gwamnatin Buhari ta yi wa yankin Neja Delta da sauran sassan kewayen ta.

Ya ce idan ya zama shugaban kasa, Zai kammala babban titin da ya tashi daga Yankin Gabas zuwa na Yamma. Ya ce tun lokacin mulkin su shi da Obasanjo aka fara aikin, amma Buhari ya yi watsi da aikin.

Atiku ya ce zai bi abin da dokar kasa ta gindaya a cikin kundin tsarin mulki, ba zai rika yin kamar yadda Buhari ke yin kama-karya ba.

Shi ma da ya ke jawabi a wurin, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya ce tun da Buhari ya hau mulki tattalin arzikin Najeriya ke ja baya. Ya kara da cewa duk wasu ayyukan raya kasa da ke jihohin Ribas, yankin Neja Delta da Kudu maso Gabas, duk a lokacin PDP aka gudanar da su.

Sauran wadanda su ka yi jawabi a wurin sun hada Bukola Saraki, Gwamnan Ribas da Shugaban PDP na kasa, Uche Secondus.

Share.

game da Author