CUTAR DAJI: Wayar da kan mutane game da cutar ne mafita – Project Pink Blue

0

A ranar Asabar ne mutane da dama suka gudanar da tattaki daga otel din Transcop zuwa Titin Sakatariya dake Abuja domin wayar da kan mutane kan cutar daji ko kuma sankara.

Kungiya mai zaman kanta ‘Project Pink Blue’ ce ta shirya taron inda mutane suka yi tafiyar kilomita biyar a wannan ranar.

Jami’in kungiyar Runcie Chidebe yace ranar 4 ga watan Faburairu rana ce da aka kebe domin wayar da kan mutane kan wannan cuta a duniya.

” Binciken da Kungiyar kiwon lafiya ta Duniya (WHO) ta gudanar ya nuna cewa akalla mutane miliyan 24.6 na dauke da cutar sankara a duniya sannan ana rasa kashi 12.5 bisa 100 daga cikinsu.

” Hasashe ya nuna cewa a shekarar 2020 mutane miliyan 16 za su kamu da cutar sannan kashi 70 bisa 100 daga cikin su za su rasa rayukansu idan ba an gaggauta daukan mataki ba kan kawar da cutar.

Chidebe ya ce a Najeriya kuwa abin ya fi muni domin mutane da dama na rasa rayukan su a dalilin kamuwa da cutar saboda rashin samun kulan da ya kamata.

Ya ce saboda haka ne kungiyar su take yi wa mutane gwajin cutar kyauta don gano cutar da wurin na taimaka wa wajen ceto rayukan mutane.

Bayan haka Chidebe ya yi kira ga mutane da su kula da irin abincin da suke ci ganin cewa rashin cin abincin da ya kamata na daga hanyoyin kamuwa da cutar.

” Zukar tabar sigari, shan giya, rashin motsa jiki, rashin cin abincin dake kara karfin garkuwan jiki na cikin hanyoyin kamuwa da cutar.

A karshe Chidebe ya yi kira ga gwamnati, masu fada a ji da sauran mutane da su hada hannu da gwamnati domin wayar da kan mutane musamman mazauna karkara game da cutar.

Ya ce haka zai taimaka wajen hana yaduwar cutar a kasar baki daya.

Share.

game da Author