COPA DEL REY: Za a gwabza tsakanin Barcelona da Real Madrid

0

Valverde mai horas da ‘yan wasan Barcelona ya shiga damuwar tunanin ko Leonel Messi ba zai iya buga wasan farko na Gasar Kofin Copa Del Rey da kungiyar sa za ta kara da abokiyar adawar ta, Real Madrid a ranar Laraba mai zuwa ba.

Za su hadu ne a wasan kusa da na karshe a karo na farko a filin Camp Nou na Barcelona.

Messi ya ji ciwo ne jiya Asabar a wasan su da Valancia, wanda aka tashi 2:2 a filin Camp Nou.

Wasan bai yi wa Barcelona dadi ba, saboda ya rage mata ratar da ke tsakanin ta da Atletico Madrid wadda ke ta biyu da kuma Madrid, wadda ke ta uku.

A yanzu maki 6 ne tsakanin Barcelona da Atletico, kuma Atletico na da wasa daya da za ta buga da Real Betis a yau Lahadi.

Gasar Copa Del Rel ta nuna cewa Barcelona ta dogara da Messi ne, ganin cewa wasanni biyu da ta buga a zagayen farko da kungiyoyin Levente da Sevilla, duk shan kashi ta yi.

Sai a zagaye na biyu ne ta yi nasara a kansu, bayan ta saka Messi a wasan.

Haka wasan ranar asabar na La Liga da ta buga da Valencia, tun farkon wasa ne aka sheka wa Barcelona kwallaye biyu.

Shigo da Messi ya sa kungiyar ta rama kwallayen da aka sheka mata. Sai dai kuma Messi ya fara dingishi bayan cin kwallo ta biyu da ya yi.

Ya fita fili an duba masa kafar, daga baya ya koma ya ci gaba da wasa, har aka tashi.

Mai yiwuwa Valverde bai cire Messi ba ne, saboda ya so ya yi nasara sosai a kan Valencia. Domin bai yi tsammanin za a shammaci Barcelona a zura mata kwallaye har biyu a farkon fara wasa, kuma a gida ba.

To sai dai kuma wata barazana da Valverde ke tsoro, ita ce idan likitoci su ka bada shawarar kada Messi ya buga wasan su da Madrid a ranar Laraba mai zuwa a Camp Nou.

Valverde ya ce don Madrid ba ta yawan cin kwallaye birjik a wannan kakar wasa, bai yiwuwa a yi sako-sako da kungiyar, domin a ko da yaushe Madrid dai Madrid ce, ba a sha mata alwashi, sai an tashi.

Masu lura da wasanni na ganin cewa ko da Madrid ta yi abin a zo a gani a Camp Nou, to Barcelona za ta iya rama wa kura aniyar ta, har gida a filin Santiago Barnabueu.

Share.

game da Author