Shugaban kotun Da’ar Ma’aikata CCT, Danladi Umar ya umarci Sufeto Janar din ‘yan sanda da shugaban hukumar Tsaro na SSS su taso keyar dakataccen Alkalin Alkalan Najeriya Walter Onnoghen a duk in da yake a fadin Kasar nan.
Idan ba a manta ba kotun CCT na tuhumar Onnoghen ne bisa karya doka da yayi na kin bayyana kadarorin sa duka a lokacin da ya zama Alkalin Alkalan Najeriya.
An bankado wasu Kadarori na miliyoyin naira da ya killace su ya ki bayyana su. Wannan zargi da ake yi wa Onnoghen ya tabbata bayan shi da kan sa ya amince ya tafka kuskure wajen kin bayyana wasu daga cikin kadarorin sa.
Tuni dai shugaban Kasa Muhammadu Buhari har ya nada sabon babban mai shari’a na kasa.
Alkalai da wasu ‘yan siyasa sun nuna rashin amincewar su da wannan abu da gwamnatin Buhari ta yi sai dai kuma wasu da dama sun bayyana cewa abin da shugaba Buhari yayi daidai ne bai saba wa dokar kasa ba.
An bukaci Onnoghen ya bayyana a CCT amma yaki, inda alkali mai kare sa ya nemi kotu ta dakatar da ci gaba da sauraren karar saboda bata da hurumin sauraren irin wannan tuhuma.
Yanzu dai kotun CCT ta bada umarnin a kamo mata Onnoghen a duk inda ya ke a fadin kasar nan.