Buhari zai binciki yadda gwamnatin Obasanjo ta kashe dala biliyan 16 na hasken lantarki

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya roki jama’a su sake zaben jam’iyyar APC domin ta sake samun damar karin shekaru hudu da za ta kammala dukkan ayyukan cigaban kasa da ta fara samarwa.

Buhari wanda ya yi wannan bayani a wurin kamfen din APC a Abuja, ya ce wannan gwamnati na bukatar lokacin da za ta cigaba da yin amfani da kalilan din kudaden da ta ke samu domin kara samar wa jama’a ayyukan raya kasa.

Ya kara yin alkwarin inganta rayuwar al’ummar kasar nan idan aka sake bas hi damar zama shugaban kasa na shekaru hudu masu zuwa a zaben da za a gudanar jibi Asabar.

Ya ce sun samar da abubuwa da dama, akwai wasu kuma da ake kan hanyar samarwa, kamar titinan jirgi da sauran su.

“Idan ku ka kara mana damar wasu shekaru hudu, to ina tabbatar muku da cewa ba za ku yi da-na-sani ba.” Inji Buhari.

Daga nan kuma sai ya ce a shekarun gwamnati can baya an almubazzarantar da dala bilyan 16 da sunan inganta hasken lantarki. Don haka duk wanda aka samu da hannu, to za a gurfanar da shi a kotu.

Duk da dai Buhari bai ambaci sunan wadanda ake zargi da aikin hasken lantankin ba, to an faro aikin ne a lokacin gwamnatin Olusegun Obasanjo.

Buhari yace tunda babu kudin kuma babu aikin da aka yi da kudaden don haka za a yi bincike.

Buhari ya roki kasashen Turai da su bada hadin kai wajen dawo da dukiyar Najeriya da ke can damfare. Ya ce wadannan dukiya na taimakawa wajen gudanar da ayyukan more rayuwa a kasar nan.

A yau Alhamis ne Buhari zai kammala rangadin neman zaben sa a Katsina, jihar sa.

Share.

game da Author