Buhari ya yi juyayin kashe-kashen da aka yi a Kaduna da Sokoto

0

A yau Laraba ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana juyayin sa bisa kashe- kashen rayuka da aka yi a a garin Kajuru jihar Kaduna da kuma harin da akai wa wasu kauyuka a jihar Sokoto.

Mai taimaka wa Buhari kan harkokin yada labarai Garba Shehu ya sanar da haka a Abuja.

Buhari yace rasa ran dan Najeriya daya tal daidai yake da mutuwar rayukan mutane da dama a kasar.

Ya kuma jadadda cewa nan ba da dadewa ba wadannan ayyuka na mahara da tashe-tashen hankula zai zama tarihi.

El-Rufa’I ya yi ganawar siri da Shugaban kasa Buhari

A jiya Talata ne gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai yayi ganawar sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar gwamnati.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriyata ruwaito cewa gwamnan ya yi wannan ziyarar gaggawa ne domin yi wa Buhari bayanin abubuwan dake faruwa a jihar Kaduna game da rikicin garin Kajuru.

An kashe mutane 29 a Kajuru –‘Yan sanda

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna Ahmad Abdur-Rahman ya bayyana cewa mutane 29 ne aka rasa a harin da aka kai wasu kauyukan karamar hukumar Kajuru.

Abdur-Rahman ya fadi haka ne bayan wasu mazauna kauyen sun bayyana wa PREMIUM TIMES cewa an birne akalla mutane 30 bayan harin da aka kai.

Duk da cewa ‘yan sanda sun kawo wa mutanen garin dauki a lokacin da aka kai wannan hari, sai da wani dansanda daya ya samu rauni.

Abdur-Rahman ya ce maharan sun bi gida gida suna kashe mutane sannan suna koona gidajen.

Abdulrahman ya ce an kashe mutane 29 ne sannan an kona gidaje sama da 40.

An kashe mutane 16 a arangamar mahara da ‘yan banga a jihar Sokoto

Kakakin ‘yan sandan jihar Sokoto Muhammad Sadiq ya bayyana cewa wasu mahara sun kashe mutane 16 a karamar hukumar Raba.

Sadiq ya bayyana haka wa PREMIUM TIMES a daren Talata inda ya kara da cewa maharan sun far wa kauyen Yawuri dake karamar hukumar Raba da misalin karfe biyu na safiyar Talata inda suka yi garkuwa da mutane shida a kauyen.

Wadanda akayi garkuwa da sun hada da Ayuba Tali, Mamman Yawuri, Musa Usman, Kamusho Yawuri, Atta Yawuri da Illiya Tali. Ba a dade da tafiya dasu Illiya Tali ya sulale ya gudu daga inda aka ajiye su.

” Bayan gari ya waye wasu ‘yan banga dake kauyen suka fantsama dajin domin nemo wadannan mutane. An yi barin wuta tsakanin maharan da ‘yan banga inda har aka kashe mutane 16.

Sadiq yace akwai yiwuwar cewa sauran raguwar maharan da suka tsere daga jihar Zamfara ne shigo wasu sassan jihar sokoto din.
Ya ce duk da haka rundunar za ta yi iya kokarin ganin ta kamo wadannan mutane.

Share.

game da Author