Buhari ya nuna alhini kan wadanda suka mutu a tirmitsitsin taron APC a Fatakwal

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna jimami, alhini da kuma ta’aziyyar rashin wadanda su ka mutu a tirmitsitsin kamfen na jam’iyyar APC a Fatakwal.

Tirmitsitsin dai ya faru ne jiya Talata a babban birnin na jihar Rivers a wurin gangamin taron APC a Fatakwal inda aka bada rahoton mutuwar wasu mahalarta kamfen din.

Sahara Reporters ta ruwaito cewa mutane hudu sun mutu, wasu da dama kuma sun samu raunuka.

Sai dai kuma ita dai Fadar Shugaban Kasa ba ta bayyana adadin wadanda suka rayukan na su ba.

Cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai na Fadar Shugaban Kasa ta fitar, Garba Shehu ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya na mika ta’aziyya da ‘yan uwa da abokan arziki na wadanda suka rasa rayukan su a Fatakawl jiya.

Ya kuma nuna rashin jin dadin yadda aka rasa rayuka a filin taron, duk kuwa da irin nnasara da taron na Fatakwal ya bayar, da ke nuna cewa fitar nasara ce.

Buhari ya ce da an bi a tsanake wajen ficewa da filin kwallon, to da ba wanda zai koma gida da wani rauni, ballantana har a kai ga rasa rayuka.

Mutuwar da jama’a suka yi a taron APC a Fatakwal, ta zo ne bayan sati daya da ras rayukan mutane takwas a taron APC na jihar Taraba, kuma wasub da dama suka samun raunuka.

An dai danganta abin a kan rashin kyakkyawan tsarin wurin kamfen da jam’iyyar keyi.

Makonnin biyu da suka gabata ma munbari ya rifta da wasu jiga-jigan APC a Jihar Kebbi.

Share.

game da Author