Tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya sha kayi a karamar hukumar sa ta Madobi inda shugaban Kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyar sa ta PDP suka kayi raga-raga da jam’iyyar PDP da dukka ‘yan takaran ta a zaben shugaban Kasa, Majalisar dattawa da na wakilai.
APC ta sami kuri’u 26,110, PDP ta samu kuri’u 13,113 a zaben shugaban kasa.
A zaben sanata APC ta samu kuri’u 22,731 sannan PDP ta sami kuri’u 15,913.
Sai dai kuma jam’iyyar PDP ce ta lashe zaben shugaban Kasa a mazabar da Kwankwaso ya kada kuri’a.
Discussion about this post