Jirgin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dira a garin Katsina ranar Juma’a da rana.
Gwamnan Jihar Katsina Aminu Masari da wasu Sanatoci ne suka tarbe sa a filin jirgi na Katsina Inda bayan ‘yar kwarya-kwaryar maraba da aka yi masa sai ya zarce garin Daura.
Buhari ya tafi garin Daura ne domin jefa kuri’ar sa a zaben shugaban Kasa da na majalisar Kasa da za a yi ranar Asabar 23 ga watan Fabrairu.
Hukumar Zabe Mai zaman kanta ta dage zaben kasa ne da za ayi a makon da ta gabata a bisa rashin Kammala shiri da bata yi ba.
Wannan dage Zabe da aka yi ya tada wa mutanen kasa da dama hankali Inda Jam’iyya mai mulki da ta Adawa duk sun rika sukan juna bisa wannan dage Zabe da aka yi.
Jam’iyya mai mulki wato Jam’iyyar APC ta rika cewa PDP ce ta shirya magudi da ya sa aka soke zaben.
Shugaban kasa Buhari ya fito da kakkausar murya, yana mai gargadin Hukumar Zabe da ta tabbata anyi Zabe Mai aminci a kasarnan a sabon ranar da ta gindaya.