Buhari ya Caccaki Hukumar Zabe, ya koma Abuja daga Daura

0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nuna rashin jin dadin sa ga hukumar Zabe game da dage zabe da hukumar tayi.

A jawabi da yayi wa manema labarai a garin Daura, Buhari ya ce abin takaici ne hakan da ya faru cewa hukumar INEC ba ta kyauta wa ‘Yan Najeriya ba.

” A kullum hukumar na fadi mana cewa ta kammala shirye-shiryen ta zabe kawai take jira. Ashe ba haka bane. Wani abu kuma shine kokari da gwamnati ta yi na kin saka mata baki a harkokin ta sannan kuma gwamnati ta tabbata ta bata duk kudaden da take bukata amma sai da ta gaza.

” Abu daya da nake so in jawo hankalin hukumar akai shine, ta tabbata takardun zabe da aka riga aka aika jihohi, da wadanda aka rarraba ba su fada hannun mutanen da ba nagari ba. Sannan kuma duk abubuwan da ya sa aka samu wannan matsala ba su sake faruwa ba a ranakun da ta tsayar za a yi zaben.

Kuma ya kara da kira ga yan Najeriya da su yi hakuri, kada su karaya duk da cewa baya ga tafiye-tafiye da aka yi domin kada kuri’a da kuma shigowar masu -sa-ido da ga kasashen waje, hakan bai yi masa dadi ba ko kadan.

Bayan nan Shugaba Buhari yayi kira ga ‘Yan Najeriya da su zauna lafiya da juna sannnan su gujewa yin abin da zai tada zaune tsaya.

Daga nan sai Buhari ya tashi zuwa Abuja domin halartar ganawar da hukumar zabe za ta yi da jam’iyyu da wasu ‘yan Najeriya.

Share.

game da Author