BUHARI: Sara Da Sassaka Ba Ya Hana Gamji Toho

0

Nasarar da Shugaba Muhammadu Buhari ya samu inda ya lashe zaben shugaban kasa karo na biyu a 2019, ba ta zo da mamaki ba, kuma a wani fannin za a iya cewa ta zo da mamaki.

Buhari ya samu kuri’u sama da milyan 15,000,000, shi kuma dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya samu kuri’u sama da milyan 11,000,000.

Ratar da ke tsakanin Buhari da Atiku ta kusa kuri’u milyan 4. Hakan ya nuna cewa ya fi ba Atiku ratar kuri’u kenan a wannan zabe na 2019, fiye da ratar da ya ba Goodluck Jonathan a zaben 2015.

ABUBUWAN DUBAWA GAME DA NASARAR BUHARI

Rikita-rikitar da ta dabaibaye jam’iyyar APC tun daga zaben shugabannin jam’iyya har zuwa zaben fidda-gwani, ba ta hana Buhari yin nasara ba.

Ficewar da wasu da dama suka yi daga jam’iyyar APC saboda rashin adalcin da aka yi musu, da kuma ficewar manyan jam’iyyar daga cikin APC, bai gurgunta yiwuwar sake cin zaben Buhari ba.

Mummunar matsalar garguwa da mutane da ta addabi jihohin Kaduna, Zamfara da Katsina har ma da Sokoto, ba ta hana Buhari samun kuri’u masu yawa a yankin ba.

Kashe-kashen kabilanci da ya buwayi Kudancin Kaduna, Filato dakuma rikicin makiyaya da manoma a tsakiyar Najeriya, ba su hana Buhari samun kuri’u a wadannan yankuna ba.

Duk da korarin da Kanawa suka rika yi cewa Buhari bai yi wa jihar ayyukan a-zo-a-gani ba, hakan bai hana su yi masa ruwan kuri’u ba.

Duk da ita kan ta jihar da Buhari ya fito, wato Katsina ba ta ci gajiyar ayyukan gwamnatin Buhari sosai ba, hakan bai hana Katsinawa zuba masa kuri’a ba.

Jigawa ta zuwa masa kuri’a duk kuwa da cewa ita ma ana ganin ganin ba ta ci moriyar gwamnatin Buhari kamar yadda ya kamata ba.

Jihar Zamfara ma ba ta dubi yawan kashe-kashen su da masu garkuwa key i ba a matsayin wani laifin gwamnatin Buhari. A wannan karo sun kara zuba masu kuri’u.

Yawan taron jama’ar Kwankwasiyya a jihar Kano bai amfana wa Atiku da PDP komai ba. kowa ya yi tsammani za a yi kankankan tsakanin Atiku da Buhari a Jihar Kano. Kuri’u 300,000 da PDP ta samu a Kano, abin kunya ne, ba abin tinkaho ba ne.

Duk da cewa Buhari bai samu kuri’u da yawa kamar yadda ya samu a jihohin Kaduna, Kano, Katsina, Jigawa da sauran Jihohi a Arewa ba kamar yadda ya samu a 2015, hakan bai sa ya fadi zabe ba.

Buhari ya samu karin kuri’u ne a wasu Jihohin da ba Arewacin kasar nan ba, albarkacin manyan ‘yan jihar da ke kan manyan mukaman gwamnatin tarayya.

Yankin jihohin Kudu Maso Gabas da Peter Obi, mataimakin takarar Atiku Abubakar ya fito, ba su zuwa wa PDP kuri’un da za a san cewa da gaske suke yi wajen neman shugabanci ba.

Kuri’un da Atiku ya samu a jihohin kabilar Igbo kakaf, ba su kai yawan wadanda Buhari ya samu a Jihar Kano ba. Kuma ba su kai wadanda ya samu a jihar Katsina ba.

JIHAR LAGOS ta kunyata jam’iyyar APC. Duk da bimbin amfanar da suka yi da mulkin Buhari fiye da dukkan sauran jihohin kasar na, kuri’un da APC ta samu a jihar ba su kai yawan wadanda ta samu a zaben 2015 a jihar ba.

A jihar Lagos Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya fito. A can jagoran APC, Bola Ahmed Tinubu ya fito, kuma a can Minista mai rike da ma’aikatu uku shi kadai, Raji Fashola ya fito. Amma kuri’un da Buhari ya samu a Lagos ba su kai 600,000 ba.

Kada a manta cewa Tinubu ya yi wa Buhari alkawarin samun kuri’u milyan uku a jihar Legas.

Har yanzu dai akwai rashin gamsuwa da yadda shugabanni ke mulki a kasar, shi ya sa mafi yawan jama’a bas u damu da zuwa jefa kuri’a ba.

Mutane milyan 84 suka yi rajistar zabe, amma milyann 73 ne suka karbi katin rajista.
Daga cikin milyan 73 masu rajista a hannu, wadanda suka yi zabe ba su wuce milyan 17,000,000 kacal ba.

Sama da mutum milyan 50 kenan sun yi kwanciyar su gida, a bisa ra’ayin cewa ‘kowa wa inna ta aura, to baba ne!’

Wandanda suka yi zabe a 2019 ba su kai yawan wadanda suka yi zabe a 2015. Wannan na nuni da cewa jama’a su na ci gaba da fidda rai daga samun ingantacciyar rayuwa daga shugabannin da suke zabe.

Saura da me? Zargin an tabka magudi da kuma kashe-kashe da tashe-tashen hankulan da suka haifar da lalata kuri’u, yin aringizo, kwange, amfani da kudade da hana wasu yin zabe kuwa, wannan matsala ce da kotu kadai za ta iya yanke hukunci, ba marubuta ra’ayoyi ba.

Share.

game da Author