Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ba mutum bane da dole-dole sai ya ci gaba da zama a kujerar mulki.
Oshiomhole ya yi wannan bayani ne jiya Laraba a taron da ya yi da manema labarai a Abuja, inda ya bayyana musu cancantar Buhari na sake tsayawa takarar shugabancin kasar nan.
Ya ce Buhari ya na bukatar wasu shekaru hudu domin ya ci gaba da kokarin da ya fara na sake gina Najeriya.
Ya ce tunda dokar kasa ta ba shi damar sake tsayawa takara, to ya cancanta a sake zaben sa domin shi ne zai iya kai Najeriya zuwa matakin cigaba, wanda a jam’iyyance su ke kira ‘Next Level’.
Oshiomhole ya ce Buhari ba mutum bane da dole-dole sai ya ci gaba da zama a kujerar mulki ba. Ya yi alkawarin gudanar da sahihin zabe. Kuma idan ya yi nasara, to zai kara kai kasar nan matakin nasarar kayan more rayuka da inganta tattalin arziki.
Daga nan sai ya ce idan an je zabe ranar Asabar, to a zabi APC, kuma a tuna abubuwan da dan takarar ahugaban kasa a karkashin PDP, Atiku Abubakar ya rika furtawa a wurin kamfen.
Ya ce Atiku ya ce zai saida wasu kadarorin gwamnati, zai yafe wa wadanda suka wawuri kudade, ya la’anci ‘TraderMoney, kuma ya ce zai sake fasalin kasar nan.
Oshiomhole ya ce Buhari ya yi kokari wajen dakile Boko Haram, gina titinan jirgin kasa, hanyoyin mota da inganta hasken lantarki.
Da ya koma kan masu sa-ido daga kasashen waje, ya ce za a ba su cikakkar kariya, za a bar su su gudanar da aikin su ba tare da tarnaki ko dabaibayi ba.
Sai dai ya ce su ma su fahimci Najeriya kasa ce mai ‘yancin kan ta, kamar na su kasashen da suka fito. Don haka yin katsalanadan a lamurran cikin wata kasa, ba fa aikin su ba ne.