Wannan hari shine hari daya da yafi kazanta a hare-haren da Boko Haram suke ke kaiwa kauyuka da garuruwan jihar Barno.
A wannan hari daya kacal, an kashe mutane akalla 60 sannan sun babbake gidaje sama da 100 da ya hada da rumfanar yan gudun hijra.
Kungiyar jinkai na Amnesty International ne ya bayyana haka a rahoton ta da ta fitar inda tace ta sami wannan bayani ne daya hotunan da aka dauka da kololin sama.
Wadannan hotuna sun nuna irin ta’addancin da Boko Haram suka yi a ranar Larabar da ta gabata.
An bayyana cewa da dama daga cikin mutanen wannan yanki sun arce zuwa kasar Kamaru ganin cewa dama garin Rann na yi. Iyaka ne da kasar Kamaru.
Wani mazaunin garin ya shaida wa AI cewa matsalar ita ce saida sojoji dake aiki a garin suka tashi daga gari sanna a washe gari kuma ‘yan Boko Haram din suka far wa kauyen.
” Idan ka gudu ma baka tsira ba domin zasu bika su harbe. Dayawa an harbe su a kokarin gudu ne.
Wasu ‘Yan banga da ga kasar Kamatu da suka tsallako sun shaida wa AM cewa sun sun gamu da gawarwakin mutane a hanya sannan sojojin da suka iske bayan sun iso garin sun shaida musu cewa sun rufe wasu 49 da aka kashe.