Boko Haram na nan daram dam a garin Baga – Inji ‘Yan gudun Hijira

0

Wasu ‘yan gudun hijira kuma mazauna garin Baga dake jihar Barno sun bayyana cewa garin Baga na nan a hannun Boko Haram.

Mazauna garin sun ce ba zama ba kadai har kula da shige da ficen duk wani mazaunin garin suke yi.

Idan ba a manta ba a ranar 11 ga watan Janairu PREMIUM TIMES ta rawaito cewa dakarun sojin Najeriya sun kwace garin Baga daga ikon Boko Haram.

Bisa ga wannan rahoto kakakin rundunar Sojin Najeriya, Sani Usman ya ce dakarun sojin sun yi nasarar kwato garin na Baga ne bayan batakashi da suka yi da Boko Haram inda suka kashe Boko Haram da dama sannan an rasa sojoji biyu.

Sai dai bayan makonni biyu da fadin haka mazaunan suka ce akwai sake a wannan domin kuwa sun gani da idanun su cewa Boko Haram na nan daram dam a garin Baga.

Wani manomin mai suna Baba Inuwa ya tabbatar da haka inda ya bayyana cewa Boko Haram sun tare dukkan wani mashiga da za ka iya shiga garin inda sai sun caje jikin mutum sannan suke bari ya shiga.

Baba Inuwa ya ce Boko Haram sun tabbatar wa mutanen garin cewa baza su kashe su ba, idan mutum zai zauna ya zauna idan kuma a’a ya tattara kayansa ya fice daga garin.

” Idan Mutum ya gaya musu cewa ba zai iya zama karkashin ikon su ba, sukan rakashi har gidan sa ya kwashe kayan sa sannan su raka shi bakin gari inda zai hau mota ya yi tafiyar sa. Bayan haka sun tabbatar mana da cewa da gwamnati su ke hari ba mu ba.

Shi ko Modu Muhammed wanda dan kasuwa ne ya ce batakashin da Sojoji suka yi da Boko Haram ya faro ne tun a ranar Laraba da karfe biyar na yamma. ” Da yawan mu mun arce ne a dalilin wannan wuta da suka bude wa juna a wannan rana. Mun boye ne a bayan garin Baga inda washe gari ranar Alhamis a inda muke boye muka ga wasu mutanen garin tare da sojoji sun fallo suma kowa na ta kansa.

Muhammed ya ce bayan ‘yan kwanaki sojojin Najeriya sun dawo amma ko da suka dawo din tsohon shingen su dake Mile -4 ne kawai suka iya kwacewa daga hannun Boko Haram.

” Boko Haram sun zama hukuma a garin Baga domin ba a shiga ko fita ba tare da izinin su ba.

Da aka tambayi Muhammed ko sojoji na da masaniyya game da abin dake faruwa a garin Baga, Muhammed yace su dai kan shiga garin Baga ne ta wani hanyar bayan gari dake tsakanin kauyukan Monguno da Kauwa.

” Idan ka biyo ta hanyar Kauwa za ka ga shingen sojoji a Mile -4 da sojoji kuma a wurin amma daga hannun ka na dama a kan hanyar Kauwa akwai wata sataciyyar hanyar da muke bi zuwa garin Baga.

A karshe da yake ganawa da PREMIUM TIMES jami’in hulda da jama’a na rundunar sojin Najeriya Onyema Nwachukwu yace babu alamun gaskiya a duk batun da mutanen ke yi game da garin Baga.

Nwachukwu yace fadin haka na daya daga cikin dabarun da Boko Haram ke amfani da shi domin mutane su tausaya musu.

” Ina tabbatar muku cewa garin Baga na nan hannun ‘Operation Lafiya Dole’ sannan rundunar na nan na gudanar da bincike a garin da kauyukan dake kusa da garin domin hana Boko Harma din sake shigowa garin.” Inji Nwachukwu

Nwachukwu ya yi kira ga mutane da su yi watsi da wannan maganar domin garin Baga baya hannun Boko Haram.

Share.

game da Author