Tsohon gwamnan Jihar Legas Kuma jigo a Jam’iyyar APC Bola Tinubu ya bayyana cewa ‘yan Najeriya ba su fahimci shugaba Buhari bane cewa da yayi duk Wanda ya saci akwatin Zabe jami’an tsaro su bindige shi.
Tinubu ya Kara da cewa a wannan lokaci da kowa ke a harzuke za a rika yi wa maganganu da dama munanan fassara.
” Babu shugaban da zai fadi cewa a kashe mutanen kasar sa. Abinda yake nufi shine duk Wanda aka Kama ya sace akwatin zabe zai dandana kudar sa. Amma ba wai a kasheshi ba. ” Inji Tinubu
Ya Kara da cewa bisa ga dokar zabe hukuncin duk wanda aka kama yana batawa ko kuma sace akwatin zabe a lokacin zabe shine daurin kurkuku na tsawon shekara biyu amma ba kisa ba.
A yau Litinin ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargadi masu shirin tada rikici da sace akwatunan Zabe da su canja shawara domin duk Wanda aka Kama yana kokarin yin haka zai iya rasa ransa.
Buhari ya yi wannan gargadi ne a wajen taron jiga-jigan Jam’iyyar APC da ya aka yi a garin Abuja ranar Litini.
Buhari ya Kara da cewa bai ji dadin dage Zabe da hukumar INEC ta yi zuwa mako na gaba ba yana mai cewa shugaban hukumar ya nuna gazawar sa matuka Kuma ya bashi kunya.
Duk a wajen wannan taro Shugaban Jam’iyyar APC Adams Oshiomhole, ya yi kiran da a yi wa jami’an Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC garambawul.
Discussion about this post