Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya nanata wa Shugaba Muhammadu Buhari cewa akwai bashin da ke kan sa na ‘yan Najeriya cewa, sun zuba masa ido ya gudanar da zaben sahihi kuma karbabbe.
Atiku ya yi wannan kiran ne a cikin wata wasika da ya karanta wurin taron rattaba yarjejeniyar gudanar da zabe lafiya.
An yi taron a yau Laraba a Cibiyar Taro ta Kasa da Kasa, a Abuja.
Atiku ya tunatar da furucin da Goodluck Jonathan ya yi kafin zaben 2015, inda ya ce muradin sa bai kai muhimmanci jinin dan Najeriya daya tal ba.
Daga nan sai ya yi kira ga INEC da ‘yan sanda su tabbatar da cewa ba su yi katsalandan cikin sha’anin zabe na.
Haka kuma ya yi kira ga jami’an tsaro da kada idon su ya rufe jar su rika farautar ‘yan adawa su na kullewa a kwanaki daya ko biyu kafin zabe.
Ya kuma yi kira ga Shugaba Buhari cewa ya yi iyakar kokarin sa wajen tabbatar da cewa an gudanar da sahihin zabe.
Idan ba a manta ba, kafin a fara kamfen sai da kwamitin Abdulsalami Abubakar ya gayyaci ‘yan takarar shugaban kasa, inda aka rattaba hannun amincewa a gudanar da zabe lafiya.
Sai dai kuma daga baya PDP da sauran gamayyar jam’iyyu sun yi barazanar janye sa hannayen su, a lokacin da guguwar rikicin dakatar da Cif Jojin Najeriya, Walter Onnoghen da Buhari ya yi, ba tare da tuntubar Majalisar Dattawa ba.