Bani da matsala da Kiristocin Kaduna, ni mutum ne mai kowa nashi – Inji El-Rufai

0

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa shi ba mutum bane da ke yin abubuwan sa yana duba kabila ko addinin mutumin dake tare da shi. El-Rufai ya ce babban abin da yafi maida hankali a kai shine kwarewa da cancanta.

Ya bayyana haka ne a taron tattaunawa da shugabannin addinin kirista na jihar.

” Idan maganan zaben mataimakiya ta ce, ina so in sanar muku cewa babban dalili na shine domin karfafa guiwowin mata su fito a rika damawa da su a siyasa amma ba wai don addini ko Kabila ba. Idan baku sani ba ban taba sanin Hadiza Balarabe kafin in zama gwamnan Kaduna ba.

” Tsohon kwamishinan kiwon Lafiya, marigayi Farfesa Andrew Nok ne ya fara gabatar da ita gare ni. Mun bukaci wanda zai zo ya gyara mana fannin kiwon lafiyar mu musamman a matakin farko ne sai aka kawo ta kuma ta taka rawar gani matuka.

” Ku duba irin ayyukan da muka yi a Kaduna. Mun gyara makarantu, mun gyara asibitoci, mun gina sabbi a fadin jihar. Amma ina so kowa ya sani mutum tara ne bai cika goma. Akwai inda zan yi kuskure amma kuma ina tabbatar muku cewa hakan ba da gangar bane, a matsayi na na dan Adam ne.

” Dole mu dawo mu hada kai mu zauna lafiya a tsakanin mu a jihar Kaduna. Mu yakice maganan addini da kabilanci a tsakanin mu mu duba cewa dukkan mu Halittar Allah ne da yayi mu wuri daya.

A karshe El-Rufai ya yabawa shugabannin addinin kirista da suka halarci taron tattaunawar sannan ya yi addu’ar Allah ya ci gaban da hada kawunan mu sannan ya zaunar da mu lafia a jihar Kaduna ada kasa baki daya.

Share.

game da Author