BABBAN KAMU: Darektan Kamfen din PDP ya koma APC

0

Jigo kuma Dan gaban goshin gwamnan Jihar Gombe, Ibarahim Dankwambo, sannan Darektan Kamfen din PDP a Jihar Gombe, Bello Tinka ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.

Mai ba shugaban Kasa Muhammadu Buhari shawara kan harkar yada Labarai, Femi Adesina ya bayyana haka a sako da ya fitar daga fadar shugaban Kasa.

Femi yace Tuni har Bello Tinka ya gana da shugaban Kasa a fadar gwamnati da ke Abuja.

Shi dai Bello Tinka da aka fi sani da Tinka Point ya yi suna kwarai a Jihar Gombe a dalilin kusancin sa da gwamnan Jihar Ibrahim Dankwambo.

Tinka ya zamo babban aminin gwamna Dankwambo da har yayi kokarin ganin ya gaje shi bayan ya kammala wa’adin mulkin sa a watan Mayu Mai zuwa.

Sai dai kash, hakan bai yiwu ba da ake ganin dalilin haka Tinka ya fusa ya fara kitsa yadda zai kauce daga jam’iyyar.

Tinka ya yi juyin da yaga dama a Jihar Gombe karkashin mulkin Dankwambo domin shine Mai mallakin Kamfanin gine-gine na Tinka Construction.

Wannan Kamfanin itace tafi more wa kwangilolin da gwamnatin Gombe ta bada na ayyukan gine-gine musamman hanyoyi a Jihar.

Wannan Kamfanin na Tinka ta girma da yanzu haka har manyan kwangilolin gwamnatin Tarayya take yi.

Idan ba a manta ba Gobe Asabar ne shugaba Buhari kuma Dan takarar shugaban Kasa a inuwar jam’iyyar APC zai ziyarci Jihar Gombe.

Wannan kamu da jam’iyyar ta yi a daidai wannan lokaci abin farinciki ne matuka.

Share.

game da Author