Hukumar kidaya ta kasa (NPC) ta bayyana cewa za ta ci gaba da karbar kudin takardar shaidan haihuwa da mutuwa daga hannun mutane har sai gwamnati ta ce su dakatar da yin haka.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ‘Daily Trust’ ta wallafa cewa majalisar dokoki ta kasa ta amince wa NPC cewa daga wannan lokaci ta rika bada takardar shaidar haihuwa da na mutuwa kyauta.
Majalisar ta amince da haka ne bisa ga rahotan da asusun tallafa wa yara kanana na majalisar dinkin duniya (UNICEF) ya nuna cewa a Najeriya a cikin yara miliyan bakwai kashi 70 bisa 100 daga cikin su basu da takardun haihuwa. Sanna hukumar na karbar Naira 4,500 a kowani shaida da za a karba
UNICEF ta ce a dalilin haka yara da dama a Najeriya basu da shaidar haihuwa saboda tsawwala kudin da NPC ta yi.
Bayan haka PREMIUM TIMES ta gana da wani ma’aikacin NPC dake babbar asibitin dake Kubwa a Abuja in da ya tabbatar da cewa NPC na karbar kudi kafin ta bada takardun shaidar haihuwa da na mutuwa.
Ma’aikacin ya ce a takardan shaidan haihuwa hukumar kan karbi Naira 500 ga kowani jariri dan kasa da watanni biyu, Naira 4000 ga yaron ya wuce wata biyu zuwa shekara 17 sannan daga shekara 18 zuwa sama sai an biya Naira 10,000.
A karshe jami’in hukumar Muhammed Isah yua sanar wa PREMIUM TIMES cewa lallai ana karbar wadannan kudade amma da zaran gwamnati ta umarce su da su dakatar da karba za su daina yana mai cewa ” Idan ko ba wannan umarni suka samu ba za su ci gaba da karbar wadannan kudade babu kakkautawa daga mutanen Najeriya.