Ba za mu amince da sakamakon zaben shugaban kasa da INEC ke bayyanawa ba – Inji PDP

0

Jam’iyyar Adawa PDP, ta bayyana kin amincewar ta da sakamakon zaben shugaban kasa, wanda ba a kai ga kammala bayyana sakamakon zaben ba.

A cikin sanarwar da Shugaban Jam’iyyar PDP, Uche Secondus ya bayar, ya ce sakamakon zaben da INEC ke bayyanawa bai yi daidai da sakamakon adadin da ita jam’iyyar PDP din ta tattara daga ejan-ejan din ta a fadin kasar nan ba.

DALILAN PDP

Ana yi wa dimokradiyya barazana

“Na farko dai, muna tabbatar da cewa cibiyar tattara sakamakon zaben mu na da dukkan sakamakon zaben da aka yi a kowane akwati, kowace rumfa da ma kowace mazaba da kowace Karamar Hukuma a fadinn kasar nan. Kuma su ma masu sa-ido na kasashen waje duk suna da orijina na wadannan sakamakon.

“Saboda haka ba mu amince da sakamakon zaben da INEC ke bayyanawa ba, ba kuma za mu taba yarda da shi ba.

Baya ga wannan dalili, PDP ta yi zargin cewa an hada baki da jami’an INEC da jami’an gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da gaggan ‘yan jam’iyyar APC, an yi aringizon kuri’u, an tauye wa masu adawa da dama damar yin zabe a fadin kasar nan, musamman a wuraren da aka san PDP na da rimjayen magoya baya.

PDP ta ce duk da hannun da jam’iyyu suka sa cewa ba a yi son kai ga zabe ba, to a fili ta ke cewa jam’iyya mai mulki ta yi amfani da karfin mulki da jami’an tsaro da suka hada da sojoji, ‘yan sanda, EFCC, SSS da INEC aka rika cin zarafi.

“Yayin da sakamakon zabe ya fara fita aka ga PDP ta fara samun rinjaye, sai jam’iyya mai mulki da kuma Shugaba Buhari suka tura manyan jami’ai wurare daban-daban, domin tirsasa sauya sakamakon zaben.

“An tura Ministan Harkokin Cikin Gida Arewa maso Yamma, an tura Sakataren Gwamnati Arewa maso Gabas.

Sannan aka tura Ministan Shari’a Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas.

Zargin da PDP ta yi cewa APC ta yi wa na’urar rumbun ajiyar sakamakon zabe shigar-burtu, hakan ya tabbatar da cewa an baddala kuri’un zaben wasu mazabu da PDP din ta yi zargin an yi.

PDP ta lissafa mazabu da dama har da aringizon zargin antaya kuri’u 10,000 a Karamar Hukumar Wurno ta Jihar Sokoto.

Ta kuma yi bayanin irin hare-hare da kashe kashe da tarwatsa mazabu da ta ce an rika yi.

Ta yi korafin yadda ejan-ejan din jam’iyyar suka sha cin zarafi da kamawa idan sun yi korafin cewa ana yin zabe alhali na’urar tantancewa ba ta amfani.

PDP ta ce kama Buba Galadima da aka yi, wanda kusan shi ne ruhin jam’iyyar PDP, ya nuna yadda wani mutum daya ke da mummunar bukatar sai ya biya bukatar sa ta ko-a-ci-ko-a-mutu.

A karshe PDP ta yi kira da a gaggauta sakin Buba Galadima da sauran ejan-ejan din PDP da ke kulle a yankunan kudancinn kasar nan.

Ta ja kunnen INEC ta tsaya a kann adalci, kada ta bada kai bori ya hau.

Share.

game da Author