Ba na fargarbar faduwa zabe – Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya shaida cewa ko kadan ba ya da fargabar faduwa zabe.

Ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke jawabi a wurin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC, jiya Litinin a Abuja.

Cikin wadanda suka halarci taron har da gwamnonin APC 11.

” Na yi kewayen jihohin nan 36 da Abuja, kuma ina jin ina da isassun magoya baya a fadin kasar nan wadanda za su jefa min kuri’a.’’

Buhari ya ce duk ma irin sakamakon da zaben ya bayar, ya na so Najeriya ta kasance kasar da ake gani da kima a idon duniya.

Ya kuma yi kira ga ’yan Nanjeriya da su fito su yi tururuwar zuwa jefa kuri’a a ranar Asabar mai zuwa.

“ Mu ba za mu yi magudi a wannan zabe ba. Mu na so a ko’ina a rika ganin martabar Najeriya. Don haka a ranar zabe kowa ya zabi wanda ran sa ya fi kwantawa da shi, kuma ya ke ra’ayi.” Inji Buhari.

Daga nan kuma ya gargadi INEC da cewa kada ta yi sako-sako da muhimmancin gudanar da zabe a kasar nan.

Buhari ya ce shi dai ya san an bai wa INEC duk irin kudade da goyon bayan da ta ke bukata domin zama mai cin gashin kan ta, kuwa wadda ta dogara da ‘yancin kan ta mai zaman kan ta.

“Idan da a ce ma Majalisar Dattawa ba ta amince an bai wa INEC abin da ta ke bukata domin gudanar da zabe ba, to hukumar na da dalilin kasa gudanar da zaben har ta dage zuwa satin nan.” Inji Buhari.

Share.

game da Author