Ba mu ce a zabi Atiku ba, inji Majalisar Shari’ar Musulunci

0

Shugaban Majalisar Shari’ar Musulunci ta Najeriya, Sheikh Yakubu Musa Hassan ya karyata rahoton da ake ta yadawa wai majalisar ta zabi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar dan takaran ta.

Ga Sakon Majalisar ga ‘Yan Najeriya

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

ASSALAMU ALAIKUM,

Mun samu labari cewa wasu mutane suna zagaya jihohi suna ɓata gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari. Kuma suna fakewa ne ƙarƙashin Majalisar Ƙoli ta Shari’ar Musulunci (SCSN). Har suna cewa wai a zaɓi wani ɗan takarar jam’iƴƴar adawa a zaɓukan da ke tafe.

Babu wani lokaci da wannan Majalisa ta zauna har ta yanke shawara cewa ta dawo daga rakiyar Shugaba Buhari. Kuma wannan Majalisa ba ta taɓa zama ta yanke shawara cewa za ta marawa wani ɗan takarar adawa a zaɓukan da ke tafe ba.

Wannan Majalisa tana kira ga al’umma musamman ma manyan malamai da ƙungiyoyin Musulunci cewa su yi watsi da waccan farfaganda da mutanen suke yi. Wannan Majalisa tana yin aiki ne da kuma alaƙa da ƙungiyoyin Musulunci ta hanun malamai da wakilai da ƙungiyoyin suka tantance suka turo mata.

Muna kira ga waɗancan mutane su daina yin waccan farfaganda da sunan wannan Majalisa. Suna da ƴancin su bi duk ra’ayin siyasa da ya kwanta musu a rai ko su goyi bayan duk ɗan takara da suke so. Amma ya kamata su samu ƙarfin halin yin haka a ƙashin kansu. Kada su jingina ra’ayinsu ga wannan Majalisa ba tare da sani da amincewarta ba.

A kullum matsayin wannan Majalisa shi ne shugabanci amana ce mai nauyi. Saboda da haka tilas ne a zaɓi shugabanni masu gaskiya da amana a kowane mataki.

Sheikh Yakubu Musa Hassan
(Shugaban Kwamitin Siyasa, SCSN)

Share.

game da Author