Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Kira ga mutanen Najeriya da ma na kasar waje da su yi watsi da duk kalaman da wani ya yi na batanci game da ayyukan masu sa-ido a Zabe ko Kuma Kasashen su cewa ba da yawun gwamnati ya yi ba.
Buhari yace a matsayin sa na shugaban Najeriya burin sa shine ya ga ana zaman lafiya a kasa da kuma karrama baki da suka shigo kasar da ba su kariya, amma ba Abinda zai tada musu da hankali ba.
Duk da cewa Buhari bai ambato sunan Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, shine dai a Kwanakin baya ya bayyana cewa duka Wanda ya zo kasar nan ya yi Mana katsalandan a al’amurran kasar nan za a koma da gawar sa ne kasar sa.
Shugaba Buhari da ya fadi haka a jawabi da yayi wa ‘yan Najeriya ranar Alhamis ya Kara da yin Kira ga ‘yan Najeriya da su kwantar da hankalun su sannan a fito a yi Zabe lafiya.
Bayannan ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnatin sa za ta zuba ido ta ga cewa an gudanar da zabukkan dake tafe cikin kwanciyar hankali da lumana.
Ranar Asabar ne za a yi zaben shugaban kasa a Najeriya inda Buhari da Atiku na Jam’iyyar APC da PDP ke Kan gaba wajen ganin ko shugaba Buhari ya zarce ko kuma a rantsar da sabuwar gwamnati a Mayu.