Ba abin da nake nufi ba aka ruwaito, ina nufin Kada wasu suyi mana katsalandan a harkokin mu ne – Inji El-Rufai

0

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa ba a fahimci abin da yake nufi bane in da ya ce duk wanda ya yi wa kasa Najeriya katsalandan a harkokin zabe, yayi shirin zama gawa.

El-Rufai ya ce abinda yake nufi shine Najeriya ba za ta amince da wani ya shigo kasar nan ya yi mana katsalandan ba a harkokin mu amma ba wai yana kira bane da a yi tashin hankali ko kuma domin wanta manufa da ba na zaman lafiya ba

Idan ba manta gwamna El-Rufai ya bayyana cewa Najeriya ba za ta zuba ido ta bari wani daga kasan waje ya zo kasarnan ya saka mata baki a harkokin ta ba musamman a wannan lokaci na zabe cewa duk wanda yayi haka toh lallai ko za a koma da gawar sa ne gida.

Ya yi wannan caccakar ce a wata hira da aka yi da shi a gidan talbijin na NTA a jiya Talata da dare, a wani shiri mai suna ‘Tuesday Live’. Cyril Stober ne ya tattauna da shi.

“ Masu kiran wasu su shigo su sa-baki cikin harkokin Najerya, to a fada musu mu na jiran mu ga duk wanda zai shigo ya yi mana katsalandan. Wanda ya kuskura ya shigo, to sai dai a maida gawarwakin su a cikin buhunan daukar gawarwaki can a kasashen da suka fito.”

Samuel Aruwan da ya saka wa takardar hannu ya bayyana cewa gwamna El-Rufai bai yi nufin tunzura jama’a ba.

” Duk wanda ya iya turanci sannan ya san yadda ake tsara kalamai a harshen Turanci ya san cewa ba abin da yake nufi ba kenan. Abinda gwamna El-Rufai yake nufi shine Najeriya kasa ce mai cikakken iko da bai kamata ace wai wasu kasashe na yi mata katsalandan a al’amurorin ta ba.

” Sannan kuma yayi kira da a sa ido matuka kan zaben da za ayi domin ganin ba a shigo da kamayamaya, murdiya da coge ba a zabukan dake tafe.”

Share.

game da Author