Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa har yanzu wasu hukumomi a karkashin gwamnatin sa ba su daina karkatar da kudaden jama’a ba. Wasu kuma sun ki su rika zuba hakikanin kudaden shiga da hukumomin ke samu a aljihun gwamnati.
Buhari ya yi wannan tsokaci ne yau Litinin, a lokacin da ya ke rantsar da Hukumar Gudanarwar ICPC a fadar sa.
Buhari dai bai ambaci ko da sunan wata hukuma daya da aka kama da laifin ba, kuma bai fayyace irin hukuncin da za a yi wa shugabannin hukumomin da ke yin kwangen kudaden ba.
Ya ja kunnen Sabon shuhaban hukumar gudanarwar da ya hada kai da bangaren gwamnati, kamar ofishin Akanta Janar domin zakulo hukumomin da ba su zuba kadaden shigar su a asusun gwamnatin tarayya.
Bolaji Owasanoye ne aka nada sabon shugaban hukumar gudanarwar ta ICPC.
Owasanoye ya bayyana wa manema labarai cewa ba zai yi kasa-kasa ba wajen ganin an bankado masu wawuran kudaden gwamnati da amfani da kujerun su wajen daka dokan kasa.