Atiku ya yi alkawarin kammala aikin Dam na Mambilla cikin shekaru hudu

0

Dan takarar shugabancin kasa a karkahin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi alkwarin zai kammala aikin madatsar ruwan samar da karfin lantarki ta Mambilla Hydro Electric Power Dam, da zarar ya yi nasarar zama shugaban kasa.

Atiku ya sha wannan alwashi ne a jiya Talata yayin da ya ke jawabi a wurin yakin neman zabe a Jalingo, babban birnin Jihar Taraba.

Atiku ya ce gwamnatin Buhari ta yi alkawarin gina dam din amma ta kasa, ta kasa cika alkawarin ta.

Ya kuma alkawarin dakile matsalar tsaro a jihar Taraba da kasa baki daya.

“ Idan har ku ka zabe ni na yi nasara, to ina tabbatar maku da cewa zan kammala aikin madatsar ruwa ta samar da wutar lantarki a Arewacin kasar na, a nan Mambilla, wadda za ta gaggauta samar da tattalin arziki a wannan yanki.

“ Zan kuma gina titinan gwamnatin tarayya a jihar Taraba tare da gaggauta biyan wannan jihar kudaden da ta kashe wajen gina titinan gwamnatin tarayya, wadanda tarayyar ce ke da hakkin gina titina, ba jihar Taraba ba.”

Ya kuma yi kira ga ‘yan Taraba su sake zaben gwamna Darus Ishaku, domin ya ci gaba da ayyukan alheri na inganta rayuwar al’umma da ya ke yi.

Shugaban PDP Uche Secndus da dan takarar mataimakin shugaban kasa, Peter Obi, duk sun yi jawabi a wurin kamfen din.

Share.

game da Author