Atiku ya lashe Zaben rumfunar Zaben fadar shugaban kasa

0

Abu mai kamar da wuya ya faru a fadar gwamnati Inda sakamakon zabukan da akayi a fadar shugaban kasa sun nuna Atiku ne ya lashe zaben ba shugaba Buhari.

Akwai mazabu biyu a fadar shugaban kasa.

Atiku ya samu kuri’u 505 a rumfar PU 021, Buhari Kuma kuri’u 552.

A rumfar PU 022 Kuma Atiku ya samu kuri’u 525 shi Kuma shugaba Buhari ya samu kuri’u 465.

Da aka tattara sai Atiku ya samu kuri’u 1,030, shi Kuma Buhari 1017.

Share.

game da Author